Ciwon Lafiya

Kungiyar likitoci ‘NARD’ za ta fara yajin aiki ranar Alhamis

Kungiyar likitoci NARD ta bayyana cewa za ta fara yaji aiki ranar Alhamis mai zuwa idan har gwamnati bata biya mata bukatunta ba.

Shugaban kungiyar Uyilawa Okhuaihesuyi ya sanar da haka bayan taron kwamitin zartarwar kungiyar a farkon wannan mako.

Okhuaihesuyi ya ce kungiyar za ta fara yajin aikin ne ganin cewa wa’adin kwanakin da ta bai wa gwamnatin tarayya domin ta biya bukatunta zai cika ranar 31 ga Maris 2021.

“A dalilin haka kungiyar NARD za ta fara yajin aiki da ga ranar 1 ga Afrilu da karfe 8 na safe.

Bukatun kungiyar NARD

Okhuaihesuyi ya ce bukatun da suke neman gwamnati ta biya sun hada da biyan albashin ma’aikatan lafiya dake karkashin kungiya daga shekarar bara zuwa watan Maris 2021.

Ya kuma ce kungiyar na bukatan gwamnati ta yi karin kashi 50% na alawus din da ake biyan ma’aikatan lafiyan dake kula da masu fama cutar korona a kasar nan.

Okhuaihesuyi ya ce kungiyar na bukatan ganin cewa inshoran kare lafiyar jami’an lafiya da gwamnati ta kafa na aiki sannan a biya ma’aikatan lafiyan da suka mutu a dalilin kamuwa da cutar korona yayin da suke aikin ceton rai.


Source link

Related Articles

236 Comments

  1. Pingback: 888 casino online
  2. Pingback: apply essay
  3. Pingback: essay genorator
  4. Pingback: 1lambent
  5. Pingback: cruise gay dating
  6. Pingback: free phx gay chat

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button