Wasanni

KWALLON ƘAFA: Kofin Afrika wanda Masar ta lashe dindindin ya ɓace

An tabbatar da sanarwar ɓacewar Kofin Afrika, wanda ya zama mallakin kasar Masar, bayan da ta dauki kofin sau uku a jere.

Yayin da rahotannin farko ke nuna cewa ɓarayi ne suka arce da shi, amma daga baya dai bayanan da suka fito daga jami’an gwamnati sun ce kofin ya salwanta ne a wata gobara da aka yi, wadda ta yi mummunar barna a Hedikwatar Ƙungiyar Kwallon ƙafa ta Masar, tun cikin 2013.

Rahoton goal.com ya ce tsohon Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Kwallon ƙafa ta Masar, Ahmed Shobair ne ya ce ba a san kofin ya ɓace ba, har sai daga baya da aka zo aikin ginin dakin tarihi, wanda za a tattara kofunan da kasar ta ciwo a killace a ciki, sannan aka nemi kofin aka rasa.

“Jami’an kwamiti masu zama bayan kowace shekara biyar, kuma masu kula da Hukumar Kwallon Kafa, sun cika da mamaki yayin da suka shiga ba su ga kofin mai daraja ba.” Inji Shobair.

“Yanzu dai sun tabbatar cewa kofin ya bace, kuma za a fara kwakkwaran bincike.”

A na sa ɓangaren, tsohon dan wasan Masar, Magdi Abdelghani, ya kira taron manema labarai, inda ya yi masu jawabin cewa kofin ya ɓata tun shekaru bakwai da suka gabata.

“Bayan gobarar da ta tashi a hedikwatar ta Ƙungiyar Kwallon, kofuna sun bace. An kuma bi diddigin bincike. Cikin wadanda suka bace har da Kofin Afrika wanda muka rike mallakin kasar nan, bayan Masar ta yi nasara sau uku a jere.”

“Wasu na cewa kofin na hannun Shawky Gharib, tsohon kociyan Masar, wasu ma cewa suke yi ya na a hannun Hassan, tsohon kaftin din Masar ko.”

Duk da an kori Masar da wuri a shekarar da ta gabata da ta dauki nauyin wasan a kasar ta, ita ce dai kasar da ta fi kowace kasar Afrika nasarar lashe kofin har sau bakwai.


Source link

Related Articles

303 Comments

 1. Pingback: generic stromectol
 2. Pingback: ivermectol 12
 3. Pingback: ivermectin 3 mg
 4. Pingback: best sildenafil
 5. Pingback: viagra 100mg price
 6. I keep listening to the news lecture about receiving boundless online grant applications so I have been looking around for the finest site to get one. Could you advise me please, where could i get some?

 7. APPLY USA ESTA VISA APPLICATION ONLINE – ELECTRONIC TRAVEL AUTHORIZATION

  http://www.imagepost.com/cgi-bin/atx/out.cgi?id=173&tag=fs1&trade=https://estatousa.com/et/mis-on-esta-taotlus-esta-voi-viisataotlus-ameerika-uhendriikidesse

  [url=http://eta.ecommzone.com/lz/EPLIVE/00AXH6/06a2b3300ffdb5e7b6a856e58f158c347b/actions/redirect.aspx?url=https://estatousa.com/et/mis-on-esta-taotlus-esta-voi-viisataotlus-ameerika-uhendriikidesse]ameerika viisa
  [/url]

 8. Pingback: 2makeshift

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news