Wasanni

KWALLON KAFA: Jigawa Golden Stars ta huce kashin da ta sha a hannun Rangers akan Abia Warriors

Kungiyar ƙwallon ƙafan na Jigawa Golden Stars ta huce kashin da ta sha a hannun kungiyar Enugu Rangers a garin Dutse a makon jiya.

Rangers sun lallasa Jigawa Golden Stars da ci daya mai ban haushi a garin Dutse.

Wannan rashin nasara da ta yi ya harzuka ƴan wasan a wannan makon inda suka bi Abia Warriors har garin Aba sun lakada musu ci.

Tun kafin wasa ta yi zafi, Aba Warriors suka jefa kwallo daya a ragar Jigawa.

Sai dai hakan bai sa ƴan wasan sun karaya ba. Suka fusata suka surfafi kungiyar Aba inda a cikin minti 24 wato minti 17 bayan baya cin su ɗaya da aka yi suka farke ta, wasa ta zama, 1-1. Haka aka yi ta fama dai har aka tafi hutun rabin lokaci.

Da aka dawo, sai wasa ta koma kamar ƴan Jigawa ne ke gida ba sune baki ba.

A minti 74 sai suka jefa kwallo ta biyu a ragar Abia ta hannun Samuel Stone. Kan a sake natsawa cikin wasa sai Samuel ya sake jefa kwallo a ragar Abia Warriors.

An dai ta shi wasa, Abia na da ci 1, Jigawa nada Ci 3.


Source link

Related Articles

12 Comments

  1. I’m not that much of a online reader to be honest but your sites really nice,
    keep it up! I’ll go ahead and bookmark your site to come back later.
    Cheers

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button