KannyWood

Kyamarar tsaro ta tona asirin wani babban mutum a wata ma’aikata.

Kyamarar CCTV ta fallasa wani ma’aikacin kamfani, inda ta nuna shi a lokacin da yake tsaka da aiwatar da aikin sa na halin bera.

Gaskiya dai barawo baiji dadin halin sa ba, musamman ma wanda kake tare da kai, ka yadda da shi, idan ya ha’ince ka abin yafi ciwo.

Shek Abdallah Usman Gadon Ƙaya ya bada labarin zanba cikin aminci, da wani mutum ya aikata a kamfanin da kowa ya yarda da shi.

Shi dai mai kamfanin ya kasance kullum sai yaga an masa sata, kuma ba kadan ba. Amma ya kasa gano wanda yake masa wannan aika-aika. Lamarin da ya saka shi a cikin matsananciyar damuwa. Inda ya shiga tunanin neman mafita.

Daga karshe sai Allah Ya bashi wata dabara ta yin amfani da Kyamarar tsaro wadda ake kira CCTV. Wanda ta haka ne ya samu nasarar kama barawon.

Babban malami Shek Abdallah, ya bada labarin yanda lamarin ya kasance, bari kuma kuji bayanin daga bakin sa.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news