Labarai

Lauya ya maka INEC kotu, saboda zargin akwai dungu cikin fam ɗin takarar da Tinubu ya cike

Wani lauya mai suna Mike Enahiro-Egbah, ya maka Hukumar Zaɓe ta Ƙass, INEC kotu saboda ta ƙi ba shi cikakkun takardun bayanan da ke cikin fam ɗin takarar shugaban ƙasa wanda Bola Tinubu ya cike.

Cikin kwafen ƙarar da lauyan ya shigar ranar Juma’a, 5 Ga Agusta 2022, a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, Enahoro ya kai ƙarar INEC ce ita kaɗai.

Ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1337/2022, ta na neman kotu ta tilasta wa INEC ba shi dukkan bayanan da ɗan takarar jam’iyyar APC na zaɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya damƙa wa INEC.

Kuma lauyan ya na so INEC ta haɗa masa da dukkan kwafen takardun da Tinubu ya bayar a lokacin zaɓen sa na Gwamnan Legas, cikin 1999 da 2007.

Fam da bayanan da lauyan ke nema sun haɗa da fam mai lamba EC13A, EC 9, katin shaidar rantsuwar affidavit da Tinubu ya taɓa yi, inda ya ce takardun makarantar sa sun ɓace, da ma duk wasu takardun bayanan da Tinubu ya aika wa INEC

Lauyan ya rubuta wa kotu cewa ya aika wa INEC neman waɗannan bayanai tun a ranakun 13 da 22 Ga Yuli, kamar yadda Dokar Zaɓe ta Sashe na 29(4) ta 2022 da Sashe na 1 (1) da (3) da Sashe na 2 (6) da Sashe na 7 (4) na Dokar ‘Yancin Neman Bayanai ta 2011 (wato Freedom of Information Act) ta tanadar. Lauyan ya ce amma INEC ta yi mirsisi ba ce masa komai ba.

Lauyan ya na so kotu ta nuna idan INEC ta ƙi bayar da kwafen bayanan, to ta karya Dokar Zaɓe ta 2022, Sashe na 29(4).

Ya zuwa lokacin rubuta wannan labari dai Babbar Kotun Tarayya ba ta kai ga damƙa wannan ƙara a hannun kowane mai shari’a ba.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news