Wasanni

Mai masaukin baƙi ta kafa tarihin shan kashi a wasan farko tun 1930

A karon farko tun bayan fara Gasar Cin Kofin Duniya, mai masaukin baƙi ta sha kashi da ci 2:0 a hannun Equador.

Wannan ne karo na farko da mai masaukin baƙi ta yi rashin nasara, tun daga farkon fara gasar cikin 1930.

A 1930 dai mai masaukin baƙi Uraguay ta sai da ta kai wasan ƙarshe kuma ta yi nasarar lashe kofi, bayan ta caskara Ajentina da ci 4:2.

A Qatar 2022 dai Qatar ta sha kashi inda kaftin Enner Valencia ya saka wa mai masaukin baƙin ƙwallaye biyu.

Wannan gasar da aka fara a yau Lahadi ita ce mafi tsada kuma mafi kashe kuɗaɗe wajen ɗaukar nauyin ta.

Masu lura da harkokin ƙwallo na ganin cewa da wahala Qatar ta taɓuka abin kirki, duk da shekaru 16 da ta yi ta na ƙoƙarin gina ƙungiya da kuma bunƙasa harkokin ƙwallon ƙafa a ƙasar.

Tsohon kociyan ƙaramin kulob ɗin Barcelona ne dai kociyan Qatar.


Source link

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button