Labarai

Mai shari’a Tanko Muhammad, ya kamu da Korona, yana Dubai

Babban Jojin Najeriya, Mai shari’a, Tanko Muhammad ya kamu da Korona, sanarwar Kungiyar Lauyoyi Musulmai na kasa.

Sanarwar ya bayyana cewa mai shari’a Tanko ya kwana biyu a Dubai ana duba shi a wani asibiti dake kasar.

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 201 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Litini.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –53, Kaduna-74, Katsina-40, Rivers-11, Filato-9, Kwara-6, Bauchi-2, Ogun-2, Taraba-2, Edo-1 da Sokoto-1
Yanzu mutum 73,374 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 66,314 sun warke, 1,197 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 5,888 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 25,005, FCT –8,424, Oyo – 3,760, Edo –2,738, Delta –1,829, Rivers 3,162, Kano –1,904, Ogun–2,330, Kaduna –3,941, Katsina -1,237, Ondo –1,751, Borno –758, Gombe –1,069, Bauchi –810, Ebonyi –1,061, Filato – 4,006, Enugu –1,363, Abia – 973, Imo –688, Jigawa –340, Kwara –1,232, Bayelsa –469, Nasarawa – 562, Osun –965, Sokoto – 193, Niger – 298, Akwa Ibom – 364, Benue – 501, Adamawa – 329, Anambra – 290, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 108, Ekiti –395, Taraba- 198, Kogi – 5, da Cross Rivers – 90.

Gwamnatin Najeriya ta ce a gaggauta sake bude cibiyoyin killace masu cutar korona, ganin yadda cutar ta sake darkakar kasar gadan-gadan ba sauki.

Ministan Harkokin Lafiya Osagie Ehanire ne ya bayyana haka a wurin taron Kwamitin Dakile Cutar Korona a ranar Alhamis, a Abuja.

Ya ce yin hakan ya zama wajibi, ganin yadda korona ta sake darkakar kasashen Turai gadan-gadan, tamkar wutar-daji.

Ya ce a wannan karo kowa na da rawar da zai taka wajen ganin wannan cuta ba ta sake fantsama ta yi wa al’ummar kasar nan mummunan illa ba.

“Mun ga yadda a ‘yan kwanakin nan ake ta samun karuwar masu kamuwa da cutar korona a kullum a kasar nan. Wannan kuwa ya sa mu tunanin sake barkewar cutar a karo na biyu.

“Dalili kenan na bada umarnin a gaggauta sake bude cibiyoyin killace masu cutar korona da cibiyoyin bayar da magunguna wadanda a baya aka rufe, saboda karancin masu dauke da cutar. Kuma a sake gaggauta kai jami’an lafiya a dukkan cibiyoyin.

Kasahen Turai na ci gaba da samun adadin masu kamuwa da cutar a kullum, fiye ma da yadda aka rika samu a baya.

Kasashe irin su Ingila, Portugal da Hungary tuni sun rigaya har sun kakaba dokar zaman gida tilas, ganin yadda adadin masu kamuwa a kullum har ma ya zarce yawan irin yadda ta rika kama mutane a watannin baya.

Abin ya kara muni da kamari a Amurka, inda a yanzu adadin wadanda su ka kamu a kasar ya haura mutum milyan 15.

Minista Ehanire ya shawarci ‘yan Najeriya su dauki kwararan matakan kare kai, musamman a lokacin Kirsimeti da sabuwar shekara, domin cutar korona ba hutu ta ke dauka ko jin fashin ranar da ba a iya kamuwa da ita ba.

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya sha alwashin cewa na Najeriya na sane da irin yadda cutar ta sake barkewar sosai a Turai, kuma ana cikin shiri a kasar nan.

Ya ce duk wasu rigakafi ko maganin korona da za a sayar wa Najeriya, zai kasance sai Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ingancin su tukunna.

“Kuma ko an kawo su a nan kasar, sai likitocin mu da masu binciken magunguna sun auna sun tantance sahihanci tukunna.” Inji Mustapha.


Source link

Related Articles

55 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button