Ciwon Lafiya

MAKON SHAYARWA: Kwankwaɗar kunu ko giyar bammi ba su ƙara yawan ruwan nono – Inji Likita

Wata likita dake aiki da asibitin ‘St. Charles’ dake Urum jihar Anambra Agnes Nwoke ta yi kira ga uwaye mata da su yi watsi da wasu daɗaɗɗun abu na al’ada da ake sa mata su yi ko kuma ake faɗi wa mata wai ƙwanƙwadan kunu mai zafi Koko ko kuma giyar Bammi a lokacin da mace ke shayarwa yana ƙara ruwan nono.

Likita Agnes ta fadi haka ne lokacin da take jawabi a wurin taron ranar shayarwa na wannan shekara da aka yi a garin Awka a makon da ta gabata.

An shirya taron ne domin karfafa gwiwowin mata game da sharyar da ‘ya’yan su nono zalla akalla na tsawon watanni shida sannan da wayar da su kan wasu abubuwan al’ada da aka runguma tun a da da mata ke yi wanda basu da alfanu.

Ta ce yawaita shan Koko ko Bammi wai don a samu ruwan nono ba gaskiya bane duk ruɗu ne kawai.

Agnes ta ce shan Bammi ga mace mai shayarwa na iya sa ta kwashe da barci ta kyale ɗan cikin yunwa. Tace mace za ta iya samun isasshen ruwan nono domin shayar da dan ta idan tana cin abincin dake inganta garkuwan jiki da yawan shayar da dan ta nono akai-akai.

Ta ce ruwan nono na samuwa ne idan ‘Prolactin’ dake cikin nono na aiki yadda ya kamata.

“Prolactin halitta ce a jikin mace dake samar da ruwan nono sannan wannan halitta ya fi aiki a jikin mace da dare da kuma idan ana yawaita ba jariri nono.

Agnes ta ce yawa samun hutu a lokacin da mace ke shayarwa da yawan shan ruwa ko abinci mai ruwa-ruwa a lokacin da take da ciki har zuwa lokacin da take shayawa suma wasu hanyoyi ne dake inganta samun ruwan nono.


Source link

Related Articles

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news