Labarai

Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

Bayan dadewa da ka yi ana ta raderadin cewa wai ministan shari’a Abubakar Malami zai tsaya takarar gwamnan jihar Kebbi, yanzu dai hakan ta tabbata.

Malami ya ayyana ra’ayinsa na tsaya takarar gwamnan jihar Kebbi bayan ganawa da bangaren APC dake tare da gwamnan jihar Abubakar Bagudu.

Idan ba a manta ba akwai adawa mai tsanani tsakanin bangaren gwamnan jihar Bagudu da sanata Adamu Aliero.

A dalilin haka magoya bayan Aliero basu halarsci wannan taro da kaddamar da takarar gwamna da Malali yayi ba.

Malami ya ce ” Da ya ke na fito ne daga gidan malamai ne, ba zan fito neman abu ba sai mutane sun ga ya dace in fito takara. Bayan da suka nemi in fito takara dole na amsa kira domin haka karantarwa addini ya ke.

” Tun da kun ga dacewa na kuma kun nemi in fito takara, na amsa kira. Zan fito takara domin ku jama’ar jihar Kebbi.

Duka bangaren gwamna Bagudu sun amince da zabin Malami dantakarar gwamnan jihar na jam’iyyar APC.

Sanata Adamu Aliero na goyon bayan Sanata Abdullahi ya ya fito daga yankin Arewacin jihar. Dalilin haka ya sa suka yi hannun riga da gwamnan jihar Bagudu da yake goyon bayan minista malami da suka fito daga yanki daya.


Source link

Related Articles

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news