Labarai

MARAFAN SHELLENG HON. ABUBAKAR ISA, YA MIKA BUKATAN NEMAN KARIN GUNDUMOMIN RAYA KAR-KARA (Development Areas) A MAZABAR SA

Majalisar Dokokin Jihar Adamawa Ta Fara Shirye-shiryen Samar da Sabbin Gundumomin Raya karkara a Mazabar Shelleng da sauran kananan hukumomin jihar Adamawa.

Dan Majalisar Mai Wakkiltar Mazabar Shelleng Hon. Abubakar Isa (APC) ne ya Gabatar da Kudirin Samar da Karin Gundumomin Raya karkaran a Gaban Majalisar a Ranar Litinin.

Dan Majalisar Wanda Yake Kammala Zagayensa na biyu (2) Kuma shiya lashe Zaben Fidda Gwani na Jami’ar APC a Karo Na Uku (3) inda yake sake neman Zarcewa, ya ce an Bullo da Manufar Raya Yankunan ne domin kusantar gwamnati da jama’a Don Samar da ci Gaban kasa da Samar da Hadin kai da Tabbatar da Aminci da Baiwa Kowane dan jihar damar kasan cewa ana Damawa Dashi.

Ya Tunatar da Majalisar cewa, jihar Adamawa tana da Yankunan Raya kasa hamsin (50) inda kowace karamar Hukuma ta raba wasu Yankunan ci Gaba, Wasu Kananan Hukumomin kamar Shelleng, Yola ta Arewa, da Yola ta Kudu suna da guda daya, kuma sune mafi kanka ta aciki,

Marafan Shelleng ya kara da cewa. Kananan hukumomi kamar Fufore, Michika, da Mayo Belwa suna da mafi girma na biyar, (5) hudu,(4) da hudu(4) inda suka kasance mafi yawa aciki.

Abubakar Isa, ya nuna damuwarsa kan yadda aka samar da mazabarsa tun 1991 mai yawan jama’a kusan 200,000 da ke makwabtaka da Shani a jihar Borno a arewaci, Karamar Hukumar Guyuk ajihar Adamawa ta Yamma, Numan, Demsa, Lamurde a kudunci. Gombi da Song ta Gabas, inda suka koka da cewa duk da Yadda Mazabar Shelleng ta kasance tana da tarihi dakuma mutane daga sassan da kuma ya ruka daban-daban, Amma Yanki raya kasa daya ne kawai a fadin karamar hukumar.

“Muma muna bukatar karin Gundumomin Raya kasa kamar Yadda sauran kananan hukumomi suke dashi

Muna da mutane da dama wa’danda suke da bukatar Gundumomin, al-umman Shelleng suna da yawa don haka muna so a kara samar mana da wasu Gundumomin” inji Marafan Shelleng.

Don haka ya bukaci Majalisar da ta Zartas da kuduri don Gyara Dokar kafa kananan Hukumomi don a samar da karin Gundumomin Raya kasa dakuma ci gaba a Mazabar Shelleng da sauran kananan Hukumomin dake da bukatar kari domin baiwa al’ummar jihar dama dai-dai.

Bayan tofa albarkacin bakinsu wasu daga cikin ‘yan majalisar da suka halarci zaman sun mika nasu bukata makamancin haka.

Mataimakin kakakin majalisar kuma mamba mai wakiltar mazabar Numan Mista Pwamakeno Mackondo (PDP) wanda ya jagoranci zaman majalisar ya gabatar da kudirin karbar bukatun da Abubakar Isa ya gabatar.

Kuma an baiwa dukkan ya’yan majalisar dama bada tasu goyon baya, kuma mataimakin babban mai tsawatarwa na majalisar Mista Adwawa Donglock na Guyuk ya goyi bayan hakan

Don haka ya umurci akawun majalisar da ya sanar da kudurori ga shugabannin majalisar domin kara daukar mataki.

Marafa Dei, na daya daga cikin yan majalisa dake yawan mika bukatun al ummansu a gaba majalisar dokokin jihar Adamawa a duk lokacin Ya samu sararin yin haka.

Idan za’a iya tuna dei, a Yan kwanakin baya ma sa’nda ya mika bukatar samarwa al ummar Mazabar sa musamman ma wadanda ke AREWACIN SHELLENG yankin, Hanyoyin karkara da sauran ababen more rayuwa.


Source link

Related Articles

8 Comments

 1. I blog quite often and I really appreciate your content.
  Your article has truly peaked my interest. I’m going to take
  a note of your blog and keep checking for new details about once per week.
  I opted in for your RSS feed too.

 2. I love your blog.. very nice colors & theme.
  Did you make this website yourself or did you hire someone to
  do it for you? Plz reply as I’m looking to design my own blog and would like
  to know where u got this from. kudos

 3. wonderful publish, very informative. I wonder why
  the other experts of this sector don’t understand this.
  You must continue your writing. I’m sure, you’ve
  a great readers’ base already!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news