Nishadi

Masarautar Kano ta ɗaga darajar masallacin Jami’ar Maryam Abacha, MAAUN zuwa masallacin juma’a

Sarkin Kano Mai martaba Aminu Ado Bayero ya amince da ɗaga darajar masallacin Jami’ar Maryam Abacha MAAUN zuwa masallacin juma’a.

Shugaban jami’ar Mohammad Israr ne ya jagoranci wasu daga cikin mahukuntan jami’an zuwa fadar sarkin Kano.

Wazirin Kano Alhaji Sa’ad Mohammed wanda shine ya amshi bakuntar tawagar Jami’ar ya bayyana cewa wannan himma na jami’ar MAAUN ya zo a daidai sannan akan gaba.

” Wannan zai taimaka wa ɗalibai su rika yin sallan Juma’a a harabar makarantar mai makon yin tafiya mai tsawo a wajen makaranta.

Hakimin Kawo Alhaji Kabiru Garba wanda ya jagoranci tawagar ya ce masallacin zai samarwa ɗalibai sauki da kuma kuma mutanen dake kewaye da jami’ar.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button