Labarai

Masu layya sun karkata zuwa ga Rakuma a Kano

Bana dai kakar masu siyar da rakumi a jihar Kano ta yanke saka domin kuwa masu layya sun rika tururuwa zuwa latukan inda ake saida rakuma ne suna siya domin yin Layya gobe Asabar

A ranar Juma’a wakilin PREMIUM TIMES ya zazzagaya cikin kasuwar dabbobi dake Kofar Na’isa jihar Kano inda ya ga layin ‘yan raguna da shanu ya cika makil da rakuma.

Da yake tattaunawa da Idris Illiyasu daga jihar Sokoto dake siyar da raguna a kasuwar ya koka da rashin cinikin raguna a bana a kasuwar.

Illiyasu Wanda shine shugaban masu siyar da raguna a kasuwar ya ce bana cinikin raguna ya yi kasa sosai saboda tsada da suka yi.

Ya ce ragon da aka saida shi naira 40,000 a bara ya kai naira 60,000 a bana. Haka kuma na naira 90,000 ya kai naira 105,000 zuwa sama.

“Abin mamakin dake faruwa a bana shine yadda mutane ba su siya raguna da kamar yadda aka saba yi a shekarun da suka wuce.

“Na dade ina kasuwancin raguna amma ban taba ganin yadda farashin rago ya tashi ya yi tsada kamar a bana ba.

Haka kuma suma masu saida shanu syn koka kan yadda ciniki yayi kasa matuka.

Su ko mutane masu Layya sun ce babban dalilin da ya sa suka koma ma rakuma a bana shine, rakumi ya fi su arha

” Rakumin naira 200,000, ya fi shanun naira 500,000 ɗin da zaka siya nama. Ka ga kowa zai samu isasshen nama, a ci a yi kyuata da sadaka da shi.”


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button