Labarai

Mata ta ta fitine ni da sata a gida

Wani magidanci mai suna Mutiu Bamgbose ya roki kotun Igando dake jihar Legas da ta warware kullin auren dake tsakanin sa da matar sa a Aliyah na shekara 10 saboda tsananin son kudi da take da shi.

Bamgbose ya kuma zargin matarsa da tsafi da yawan neman maza.

“Tun da muka yi aure ba abin da Aliyah ke so kamar adai kashe kudi kawai.

“Da na gane haka sai na fara boye kudade na, amma duk da haka ban tsira ba sai ta rikide ta zama barauniya.

“Duk inda na boye kudi sai ta bi ta nemo su, kai ya kai ga har cikin saman kwanan gidana ta kan saka tsani ta shiga ko na boye kuɗi a can ciki, saboda bala’in son kuɗi.

” Tun da ta gano na daina ajiyar kudi a gida, shi kenan kuma sai tsananin gaba ya shiga tsakanin mu, sannan kuma abin haushi ma idan ta sace min kudin da saurayin ta su ke kashe wa don wulakan ci.

“Da kai na wata rana na samu saurayin na ja masa kunne game da tarayyarsa da mata ta amma duk a banza.

” Aliyah ta kwashe kaya na daga gidan mu tare ta gudu sannan ta tafi da ‘ya’yan mu ‘yan mata biyu ta bar mun da namiji.

Bayan ya saurari bayanan da Bamgbose ya yi alkalin kotun Adeniyi Koledoye ya yanke hukuncin raba auren saboda babu sauran kauna a tsakanin ma’auratan.

Koledoye ya ce Aliyah za ta ci gaba da kula da ‘ya’yan mata biyu din dake hannun ta sannan duk wata Bamgbose zai rika aika mata Naira 10,000 kudin ciyar da su.

Ya Kuma ce Bamgbose zai ci gaba da kula da dan su namiji dake hannun sa.

A duk zaman da kotun ta yi Aliyah bata zo kotu ba ko da na rana daya ba.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button