Labarai

Mataimakin gwamnan Anambra ya sauya sheƙa daga APGA zuwa APC

Mataimakin gwamnan jihar Anambra Nkem Okeke ya sauya sheka daga jam’iyyar APGA zuwa APC.

Wannan canji da Nkem yayi baraka ce babba ga jam’iyyar APGA a halin yanzu ganin ga zaben gwamnan jihar ya matso gaban goshi.

Za a yi zaben gwamnan jihar Anambra ranar 6 gawatan Nuwamba.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya kaeɓi Nkem a gidan gwamnati dake Aso Rock, Abuja.

Gwamnan jihar Imo wanda shine shugaban kamfen din zaben gwamnan jihar Anambra na jam’iyyar APC Hope Uzodinma da shugaban jam’iyyar na rikon kwarya, Mai Mala Buni.

Jam’iyyar APC ta bude wuta matuka a jihar Anambra yanzu domin a cikin wannan watan, jiga-jigan yan siyasan jihar suna ta komawa APC.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button