Labarai

Mataimakin Kakakin Majalisa ya goyi bayan gaggauta haramta baburan acaɓa a ƙasar nan

Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya Idris Wase, ya hana wani ƙudirin neman a dakatar da gwamnatin tarayya daga haramta tuƙa baburan okada a faɗin ƙasar nan.

Ɗan Majalisa Abubakar ‘Yalleman ne daga Jihar Jigawa ya miƙe ya karanto ƙorafin na sa, wanda ya ce ya na so ya zama ƙudiri.

‘Yalleman ya ce ya kamata majalisa ta hana gwamnatin tarayya haramta baburan acaɓa, har sai an samar wa jama’a hanyar sauƙaƙe masu takurawar da za su fuskanta idan an kafa dokar tuunna.

Ya ƙara da bayar da shawara cewa “idan ma tilas sai an yi dokar, to dai kamata ya yi a kafa ta yankin da ake haƙar ma’adinai, ta’addanci da kuma ‘yan bindiga.

Sai dai kuma ya na gama maganar sa sai Mataimakin Kakakin Majalisa wanda shi ne ya jagoranci zaman, ya kira shi zuwa wurin sa, inda su ka yi ƙus-ƙus, daga baya Wase ya ce akwai buƙatar a jingine hanzarin da ‘Yalleman ya kawo.

Daga nan Wase ya ce ya ga bayanan sirri da DSS su ka riƙa bayarwa har guda 44 ciki har da masu alaƙa da harin kurkukun Kuje, kuma duk sun shafi hare-hare ne na amfani da baburan acaɓa.

Ya ce baburan acaɓa hanyoyi ne na sauƙaƙe wa talakawa har da na ƙauyen su zirga-zirga. Amma lamarin tsaro ba abin wasa ba ne.

A farkon makon jiya ne Gwamnatin Tarayya ta ce za ta haramta baburan acaɓa kwata-kwata a ƙasar nan.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta na shirin haramta haya da baburan acaɓa a faɗin ƙasar nan, domin ƙoƙarin daƙile matsalar tsaro.

Ministan Shari’a Abubakar Malami ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan tashi daga taron Majalisar Tsaro ta Ƙasa, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a ranar Alhamis, a Abuja.

Malami ya ce an fahimci ana shigar wa ‘yan ta’adda da muggan makamai a maɓuyar su ne ta hanyar amfani da baburan acaɓa, shi ya sa za a hana amfani da su kwata-kwata a ƙasar nan.

Malami ya ce ya zama wajibi ‘yan ƙasa su sadaukar da wata hanyar sauƙaƙe rayuwar su, matsawar dai yin hakan zai iya magance matsalar tsaron da ta ƙi ci, ta ƙi cinyewa.

Sai dai ya ce sai an daure sosai, domin ya zama tilas gwamnati ta ɗauki matakin domin a ci moriyar tsaron da za a samar a faɗin ƙasar nan.

Malami ya ce kuma za a haramta haƙar ma’adinai a dukkan dazukan fadin ƙasar nan, domin kawar da dandazon ‘yan bindigar da ke cikin dazukan.

Da ya ke magana kan waɗanda za su tagayyara idan aka haramta amfani da baburan haya, Malami ya ce an yi nazari cewa gaba ɗaya masu amfani da baburan haya a Najeriya ba su wuce kashi 20 daga cikin mutane miliyan 206 na adadin ‘yan Najeriya ba.

Idan ba a manta ba, kwanan baya ‘yan bindiga sun kashe sojoji 30 a wurin haƙar ma’adinai a Jihar Neja.


Source link

Related Articles

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button