Labarai

Matasa sun babbake ofishin ‘Yan sanda dake Gauraka dake Tafa, titin Abuja-Kaduna

Matasa sun fasata bayan jami’an’ Yan sanda sun yi kokarin yarwatsa su a babban titin Kaduna Zuwa Abuja, wajen yin zanga-zanga ranar Litinin.

Jami’an tsaro sun yi kokarin tarwatsa dandazon masu zanga-zangar amma hakan bai yiwu ba, daga karshe dai abin ya kazanta har ya kai ga matasannsun fusata sun babbake ofishin ‘Yan sandan dake garin.

Kakakin’ Yan sandan jihar Neja, Abidun Wasiu, ya bayyana cewa tuni har an tura jami’an tsaro zuwa wannan wuri domin gudun kada tashin hankalin ya wuce haka.

Mazauna garuruwan Gauraka, Suleja, Tafa su datse hanyar Kaduna-Abuja, suna zanga zanga-zangar nuna fushin ga mahukuntan Najeriya kan yadda garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a wannan yanki.

Daruruwan matasan sun yi dafifi a babban titin bayan sun cinna wa tayoyi wuta, sannan sun hana motoci wucewa.

Wannan hanya dai ita ce hanyar da ta hada kudu da Arewacin Najeriya ta babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

Wani da ya yi magana da PREMIUM TIMES HAUSA daga wannan wuri ya bayyana cewa ko a daren Lahadi, mahara sun afka wa garin Garamu, sun waske da mutane shida.

” Sace-sacen mutane ya zama ruwan dare a wannan garuruwa namu. Kullum sai an sace mutane an nemi a biya kudin fansa. Mu dai wannan gwamnati na Buhari ta ishe mu hakannan, gwamnatin tsautsayi kawai.

Wani mai harkar sufiri, Musa, ya bayyana wa wakilin mu cewa, a dalilin haka, matasa sun hana motocin matafiya wuce ta hanyar.

” Yanzu dai ta Jere ake bi, sai a shiga ta cikin Abuja a wuce.

Idan ba a manta ba, a ranar Alhamis din da ya gabata aka sace mutum 12 a garin Madalla dake kusa da Abuja sannan aka kashe mutum daya.

Tuni dai jami’an tsaro sun isa wannan wuri inda suke ta kokarin tausa matasan su janye daga hanyar.

Yanzu dai da alama ba ‘yan bindiga ba ne kawai ke sana’ ar sace mutane, saboda sakacin gwamnati, an samu labarai masu sahihanci da ke nuna hatta yan iskan gari, makwabta, abokai da yan uwa akan hada baki da su a sace muta a garuruwa.


Source link

Related Articles

10 Comments

  1. 42891 981233This douche bag loves his illegal bretheren because hes a itiaen with the world and we need to be ashamed of ourselves I got news for you Asswipe get your asswiping ass back towards the craphole where you came from with all of your illegal beaners 350520

  2. 916619 856513Superb read, I just passed this onto a colleague who was doing just a little research on that. And he in fact bought me lunch as I identified it for him smile So let me rephrase that: Thank you for lunch! 371877

  3. 7221 392303We are a group of volunteers and opening a new system in our community. Your web internet site given us with valuable data to function on. Youve done an impressive job and our entire community is going to be grateful to you. 867694

  4. 422518 319196This style is spectacular! You certainly know how to maintain a reader amused. Between your wit and your videos, I was almost moved to start my own blog (well, almostHaHa!) Fantastic job. I really enjoyed what you had to say, and far more than that, how you presented it. Too cool! 640207

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news