Labarai

MATSALAR TSARO: Buhari ya kira Majalisar Tsaron Ƙasa zuwa taron gaggawa

Shugaba Muhammadu Buhari ya kira Majalisar Tsaron Ƙasa taron gaggawa domin tattauna batutuwan da su ka shafi tsaron ƙasa.

Cikin wata sanarwa da Garba Shehu, Kakakin Yaɗa Labaran Shugaba Buhari ya fitar, ya ce batutuwan da za su tattauna masu muhimmanci ne, “domin yanzu haka an ɗage shirin da zai ƙaddamar a Hukumar NASENI, sai wata rana nan gaba.”

Ya ce an kirawo dukkan shugabannin ɓangarorin tsaro domin a ji ƙarin bayanai daga ɓangarorin su.”

A ranar Juma’a ce Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya su riƙa sa-ido dangane da zargin da Amurka da Birtaniya su ka yi cewa ‘yan ta’adda na shirin kai hari a Abuja.

Tun bayan fitar sanarwar gargaɗin da Birtaniya da Amirka su ka yi ne, ita kuma Hukumar SSS ta ce mazauna Abuja su kwantar da hankalin su, jami’an tsaro ba za su bari ‘yan ta’adda su kai wa FCT hari ba.

Hukumar Tsaro na DSS ta ja hankalin mazauna Babban Birnin Tarayya Abuja cewa kowa ya ci gaba da gudanar da harkokin sa, kuma ya natsu.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labarai na SSS Peter Afunanya ya fitar, ya ce rundunar SSS na aiki tare da sauran ɓangarorin jami’an tsaro wajen ganin harkoki da rayuwar mazauna Abuja su na tafiya ba tare da tangarɗa ba.

Hakan ya biyo bayan wani gargaɗi ne da Ofishin Jakadancin Amurka da na Birtaniya da ke Abuja su ka fitar a ƙarshen mako, inda su ka gargaɗi ‘yan ƙasar su cewa su ƙaurace wa Abuja, domin akwai ƙishin-ƙishin cewa ‘yan ta’adda na shirin kai hari a birnin.

“Afunanya ya ce ofishin sa na shan tambayoyi dangane da gargaɗin da ofishin jakadancin Amurka ya yi na a daina shiga Abuja.”

Ya ce ita ma Hukumar SSS ta yi wannan gargaɗin cewa akwai yiwuwar neman tayar da fitina a Abuja. Amma kuma Hukumomin tsaro na bakin ƙoƙarin su.

“Yayin da SSS ke kira ga ɗaukacin jama’a su kwantar da hankalin su, hukumar na ƙara yin kira da cewa duk wanda ya ga wanin abin da ka iya zama barazana, to ya gaggauta sanar da jami’an tsaro.”

PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa ofisoshin jakadun Birtaniya da Amurka sun gargaɗin ‘yan ƙasashen su cewa su gaggauta ƙaurace wa Abuja.


Source link

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button