Labarai

MATSALAR TSARO: Gwamnonin Arewa sun goyi bayan raɗa wa Ƴan bindiga sunan ‘yan ta’adda

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, kuma Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong, ya ce a yanzu yankin Arewa na farin ciki da ayyana ‘yan bindiga cewa ‘yan ta’adda ne.

Ya ce gwamnonin yankin da al’ummar Arewa na jinjina wa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari dangane da amfani jiragen yaƙin nan samfurin Super Tucano da aka fara domin kakkaɓe ‘yan bindiga.

Lalong na magana ne da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, lokaci kaɗan bayan fitowar sa daga taron sirri da ya yi da Shugaban Ƙasa.

“Mun fara ganin ci gaba a kan wasu batutuwan da ke damun mu, waɗanda muka tattauna da shugaban ƙasa a cikin shekarar da ta gabata.

“Idan kun tuna mun kasance mun ƙagara mu ga an fara amfani da helikwaftan Super Tucano domin kakkaɓe dukkan ‘yan bindiga.

“To dama babbar matsalar ita ce amfani da irin waɗanda kayan yaƙi sai a kan ‘yan ta’adda. Saboda haka tunda a yanzu Gwamnatin Tarayya ta ayyana su cewa ‘yan ta’adda ne, yanzu sojoji za su yi masu kan-mai-uwa-da-wabi. Kuma mu a Arewa mun yi shirin a fara yi masu luguden wuta kawai. Abin da mu ke don gani kenan.” Inji Lalong.

“Don haka abin da mu ke so shi ne mu ga an fara kakkaɓe su, kuma nan da ƙarshen watanni ukun farkon shekara tsaro ya ginganta sosai, kowane ɓangaren Arewacin ƙasar nan jama’a na zaune lafiya.

Lalong ya ce lallai tilas a tabbatar da an kakkaɓe ‘yan bindiga kafin faɗuwar ruwan damana, domin ɗimbin manoma su samu walwalar shiga gonaki su yi noman su.

Ja-in-ja Da Tataɓurza Kafin Gwamnati Ta Raɗa Wa ‘Yan Bindiga Sunan ‘Ya Ta’adda:

Gwamnatin Najeriya ta ayyana wasu gungun ‘yan bindiga biyu da suka addabi Arewa maso Yammacin ƙasar cewa ‘yan ta’adda ne.

An raɗa masu sunan ne tare da duk wasu ƙungiyoyin da ke aikata wasu muggan laifuka masu nasaba da irin hare-haren da su ke kaiwa.

Raɗa wa ‘yan bindiga suna ‘yan ta’adda ya biyo bayan umarnin da Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta bayar a cikin watan Nuwamba, 2021 cewa Gwamnati ta ayyana ‘yan bindiga cewa ‘yan ta’adda ne.

Wannan sanarwa ta Gwamnatin Tarayya na cikin wata takarda da Kakakin Yaɗa Labaran Ministan Harkokin Shari’a, mai suna Umar Gwandu ya raba wa manema labarai a ranar Laraba, a Abuja.

“Wannan takarda ta zama shaidar cewa Gwamnatin Tarayya ta ayyana ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda cewa ‘yan ta’adda ne, su da duk wasu ƙungiyoyin da ke aikata ɓarna irin ta su.”

Dama a ranar 29 Ga Nuwamba ne gwamnatin tarayya ta amince za ta ayyana su da suna ‘yan ta’adda, bayan kotu ta bayar da umarni.

An yi ta ƙorafe-ƙorafen neman gwamnati ta ayyana su ‘yan ta”adda, har dai a baya Ministan Tsaro ya fito ya faɗi abin da ya hana Gwamnatin Tarayya ayyana cewa ‘yan bindiga ‘yan ta’adda ne.

A wancan lokacin, Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ba haka kawai gabagaɗi ake fitowa a ayyana cewa ‘yan bindiga su ma ‘yan ta’adda ne ba.

Ministan Harkokin Tsaro Bashir Magashi ne ya bayyana haka, tare da cewa akwai matakan da ake bi, kuma ko an bi su ɗin, to sai an tabbatar da kammaluwar su sannan za a ayyana cewa ‘yan bindiga ma ‘yan ta’adda ne.

Magashi ya yi wannan furuci a lokacin da ya kai ziyarar gani da idon irin ci gaban da ake samu a filin dagar yaƙi da Boko Haram a Barno.

Ya na tare da rakiyar Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Lucky Iraboh da sauran manyan hafsoshin ƙasa, ruwa da na sama.

Ya kuma gaba da manyan kwamandojin yaƙi na Arewa maso Gabas, wato ‘Threater Commanders’, tare da nuna gamsuwa da irin ƙoƙarin su da nasarorin da ake kan samu a yanzu.

Magashi ya yi wannan bayani ne biyo bayan tambayoyin da manema labarai su ka yi masa a Maiduguri, dangane da tsaikon da ake samu wajen ƙin kiran ‘yan bindiga da suna ‘yan ta’adda da Gwamnatin Tarayya ta ƙi yi.

Cikin makon jiya ne Shehin Malami Ahmad Gumi ya ce “za a yi da-na-sani idan Buhari ya raɗa wa ‘yan bindiga sunan ‘yan ta’adda.”

Babban malamin nan na Kaduna kuma wanda ya riƙa kurɗa-kurɗar shiga wurin ‘yan bindiga, Sheikh Ahmed Gumi, ya gargaɗi Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnatin Tarayya cewa kada su ayyana sunan ‘yan bindiga su ce musu ‘yan ta’adda.

Duk da kashe-kashe da garkuwa da mutanen da ‘yan bindiga ke yi, Gumi ya ce za a yi da-na-sani idan aka yi amfani da dokar ƙasa aka kira su ‘yan ta’adda.

Gumi wanda tsohon soja ne, kuma likita, ya daɗe ya na kamfen ɗin neman a yi wa Fulani ‘yan bindiga afuwa.

Ya shiga wurin ‘yan bindiga a dazukan Kaduna, Neja, Katsina, Sokoto da Zamfara. Kuma ya je jihohin inda ya gana da gwamnoni da gaggan gogarman ‘yan fashin daji masu garkuwa da mutane, da nufin a samu maslahar magance matsalolin da ke addabar yankunan.

Ko kwanan nan Gwamnan Katsina da na Kaduna sun nemi a bayyana ‘yan bindiga cewa ‘yan ta’adda ne, domin sojoji su samu cikakkiyar damar murƙushe su.

Sai dai Gumi a cikin wani bayani da ya wallafa a shafin sa na Facebook, ya yi babban kuskure ne idan aka bayyana ‘yan bindiga cewa ‘yan ta’adda ne.

Duk da ya nuna cewa su ma ‘yan bindiga su na kisa da ɓarnatar da dukiyar jama’a da garkuwa da mutane, to amma siyasa ta shiga cikin zukatan jama’a, musamman masu cewa su ma ‘yan bindiga ai ‘yan ta’adda ne.

Ya yi tsokaci kan yadda ‘yan bijilante ke kashe Fulanin da ba su ji ba, ba su gani ba, su ce duk ‘yan bindiga ne, abin da Gumi ya ce hakan kan tunzira sauran su shiga ƙauyuka kisan ramuwar-gayya.

Gumi ya bayyana irin ƙoƙarin da ya yi har ya sa wasu Fulani ‘yan bindiga masu yawa su ka tuba, su ka daina.

“Sai dai abin takaici, ba ni da masu taya ni wannan mawuyacin aiki da nake yi, maimakon haka ma, sai tulin masu gaba da ni na ke ƙara samu a kullum.”

Ya yi fatan a samu wani limamin Kirista na Igbo da ka Yarabawa su je su lallashi Nnamdi Kanu da su Sunday Igboho masu son ɓallewa daga Najeriya.

Ya ce idan su ka wayar wa magoya bayan su kai, za a samu maslahar zamantakewa tare da juna a matsayin mu na ƙabila daban-daban masu zaune a ƙasa ɗaya.

Ya ce malaman addini za su iya taka muhimmiyar rawa inda tsarin da babu addini ba zai iya yin tasiri ba.

Sai dai ya nuna takaicin maimakon jama’a su tashi tsaye a kwantar da wannan mummunar fitina, sai kowa ya yi zaman sa cikin ɗaki. Ya dararrashe ya na ta watsa bayanai barkatai waɗanda ba za su taɓa zama mabuɗin kawo ƙarshen fitintinu ba.

A ranar Lahadi ce dai Buhari ya bayyana cewa ‘yan bindiga da ba su da bambanci da Boko Haram.

Duk da dai har yau Shugaba Buhari bai fito ya bayyana ‘yan bindiga cewa su ma ‘yan ta’adda ne kamar yadda ake kiran ‘yan Boko Haram ba, a ranar Lahadi ya bayyana cewa “a wani ɓangaren ‘yan bindiga ba su da wani bambanci da ‘yan Boko Haram.”

Kakakin Yaɗa Labarai na Shugaba Buhari, Garba Shehu ne ya bayyana haka, a ranar Lahadi, bayan da wata mujalla mai suna The Economist, wadda ake bugawa a Landan ta buga labari cewa rashin tsaro a Najeriya ya ƙara dagulewa a ƙarƙashin mulkin Buhari.

‘Yan bindigar dai yanzu sun yi ƙarfin da har sun kai ga harbo jirgin yaƙin Najeriya ɗaya. Waɗanda Shehu ya ce sun yi ƙarfin tara kuɗaɗe da muggan makamai. “Kenan a nan ba su da wani bambanci ma da Boko Haram, waɗanda su a yanzu ma an yi masu tara-tara, an matse su a wuri ɗaya.”

‘Yan Najeriya da dama ciki har da Majalisar Dattawa da Gwamna El-Rufai na Kaduna, duk sun yi kira ga Buhari ya kira ‘yan bindiga cewa ‘yan ta’adda ne.

A martanin da Shehu ya yi masu, ya amince akwai ƙalubale daban-daban kan matsalolin tsaro a sassan ƙasar nan daban-daban.

Sai dai kuma ya ce duk Shugaba Buhari ya na ta ƙoƙarin magance matsalolin.

“Mujallar The Economist ta yi gaskiya, Najeriya na fuskantar matsalolin tsaro da dama. Sai dai a lura ba a cikin wannan gwamnatin matsalolin su ka faru ba. Wannan gwamnatin ce ma ke ta ƙoƙarin magance waɗannan ɗimbin matsalolin. “Alhali gwamnatocin baya babu wadda ta yi ƙoƙarin magance ko da matsala guda tal.” Inji Garba Shehu, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, kuma ya aiko wa PREMIUM TIMES.

Ko a cikin makon da ya gabata, sai da Gwamna El-Rufai ya goyi bayan Majalisar Dattawa Tarayya domin kiran ‘yan bindiga da suna ‘yan ta’adda.

Gwamna Nasiru El-Rufai na Jihar Kaduna ya bayyana goyon bayan sa ga Majalisar Tarayya, wadda ta yi kira ga Gwmnatin Tarayya cewa ta shaida wa duniya ‘yan bindiga su ma ‘yan ta’adda ne kawai.

El-Rufai ya ce idan aka bayyana cewa ‘yan bindiga su ma ‘yan ta’adda ne, to hakan zai ƙara zaburar da sojoji su darkake su a duk inda su ke, su na yi masu kisan kan-mai-uwa-da-wabi, ba tare da tsoron ƙorafe-ƙorafe daga bakunan ƙungiyi kare haƙƙi na kasashen duniya ba.

Gwamnan ya yi wannan furucin a ranar Laraba, a Kaduna, lokacin gabatar da Rahoton Matsalolin Tsaro Na Watanni Uku na kusa da ƙarshen shekara.

An gudanar da taron a Gidan Sa Kashim na Kaduna.

Ya na magana ne a kan ɓarnar da ‘yan bindiga ke ci gaba da yi a jihohin Arewa maso Kudu, ciki kuwa har da jihar Kaduna.

“Mu dama a jihar Kaduna mun daɗe da nuna goyon bayan a kira ‘yan bindiga da sunan ‘yan ta’adda kawai. Cikin shekarar 2017 mun rubuta wa Gwamnatin Tarayya wasiƙa mu ka nemi ta bayyana cewa ɗan bindiga fa ɗan ta’adda ne.

“Saboda sai fa an gwamnatin tarayya ya kira su da suna ‘yan ta’adda, sannan sojoji za su samu ƙarfin da za su riƙa yin shigar-kutse a cikin dazuka, su na yi masu kisan-kiyashi, yadda ƙungiyoyin ƙasashen waje ba za su riƙa yin matsin- lamba ga Sojojin Najeriya ba. Kuma ba za a ce Sojojin Najeriya sun karya dokar ƙasa-da-ƙasa ta ba.

“Don haka mu na goyon bayan matsayar da Majalisar Tarayya ta cimma, inda za mu ƙara aika wa Gwamnatin Tarayya cewa Jihar Kaduna na goyon bayan raɗa wa ‘yan bindiga sabon suna ‘yan ta’adda.

“Yin haka ne zai ba sojoji ƙarfin guiwar tashi tsaye haiƙan su murƙushe su, ba tare da wata tsugune-tashi ta biyo baya ba.”

El-Rufai ya nuna damuwa dangane da yadda a kullum ake samun rahotannin hare-haren ‘yan bindiga a jihar Kaduna, duk kuwa da irin maƙudan kuɗaɗen da jihar ke kashewa wajen samar da tsaro ga jami’an tsaro a jihar.

“Ina mai takaicin ganin yadda duk da ɗimbin kuɗaɗen da muke kashewa a ɓangaren tsaro, amma a ce har yanzu babu wata alamar raguwar hare-haren da ake kai wa jama’a a jihar.”

Daga nan sai ya roƙi gwamnatin tarayya ta ɗauki matasa 774,000, wato a ɗauki 1,000 daga kowace ƙaramar hukuma, domin ayyukan inganta tsaro a Najeriya.


Source link

Related Articles

333 Comments

 1. Pingback: 2letting
 2. Pingback: gay punk dating
 3. Pingback: mature gay chat
 4. Pingback: gay men chat rooms
 5. Howdy! Do you know if they make any plugins to help
  with SEO? I’m trying to get my blog to rank for some targeted keywords but I’m not seeing very good results.
  If you know of any please share. Cheers!

 6. Pingback: online slots free
 7. Pingback: akafuji slots
 8. Pingback: real penny slots
 9. Pingback: slots garden
 10. Pingback: free on line slots
 11. What i do not understood is if truth be told how you are not actually
  a lot more neatly-liked than you may be right now.
  You’re very intelligent. You recognize thus considerably in the case
  of this topic, made me individually consider it from so many
  various angles. Its like men and women are not fascinated until it’s
  one thing to do with Lady gaga! Your own stuffs nice.
  All the time handle it up!

 12. Yeni bir çalışma önerisi, ilaç dolabınızda çöpe atılan eski kullanılmayan reçetelerin çöp kutusuna atılmasının en az zararlı yol olduğunu söylemek.
  Geri alma ve yakma programları pahalıdır, emisyonlar
  yaratır ve pek çok insan hakkında bilgi sahibi değildir ya da bunları kullanmazlar, bu yüzden bu
  çalışma en iyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news