KannyWood

MAWAKI RARARA: Mai Arzikin Da Bai San Abin Da Yake Yi Ba

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Indabawa Aliyu Imam
Dauda Kahutu Rarara, shahararren mawaki da ya yi kaurin suna wajen kod’a ‘yan siyasa tare da aibata ‘yan adawa, ta sanadin hakan ya sami makudan kudade wanda yake barnatar da su ga wadanda ba su cancanta ba.

A yayin da dubban mutanen kauyuka a jihar Katsina jihar mawaki Rarara suka rasa matsuguninsu suke yawon gararamba suna bukatar abinci da taimako, a yayin da dubban mutane ke mutuwa da yunwa saboda rashin abinci, a yayin da dubbai ke neman taimakon daga asibiti, a lokacin ne Rarara yake hana wadannan mutane taimako yake fitar da dukiyarsa ya ba wa wadansu ashararun mutane kawai don ya sami yabo daga wajensu.

Kenan ba mu yi laifi ba idan mun ce Rarara bai san abin da yake ba, ta yadda ba ya taimakon masu bukatar taimako sai dai ya karawa masu karfi karfi. Duk yadda yake biya ake yayata taimakon da yake yi wa ‘yan film ban taba ganin labarin ya taimaki mara lafiya guda ko mai bukatar taimako ba. Akwai da masu nemawa al’umma taimako irinsu Fauziyya D. Sulaiman da sauransu da ya dace ace wannan mutumi mai suna Rarara na ba su gudummawa, maimakon ‘yan film din da kullum su kadai yake tallafawa kyautar neman yabo wacce babu lada.

Kafin mawakin ya sami daukakar da yake da ita, su ‘yan film din da kullum yake kokarin burgewa suna masa kallon bagidaje bakauye wanda bai yi makarantar boko ba, kuma har gobe suna ganin kawai gara suke wankewa, a gobe idan karayar arziki ta sami Rarara ba wani guda da za ku gani tare da shi, don haka muke kira ga Rarara da ya yi karatun ta natsu ya karkatar da taimakonsa ga mabukata ba masu lalata tarbiyar al’umma ba.

Ni ina ganin Rarara ya yi wayewar da ya kamata ya nemi yabon al’umma ba yabon masu lalata tarbiyya ‘yan film ba. A matsayinsa wanda ya tashi a karkara idan film da ‘yan film ke burge shi zai iya shiga a dama da shi ya fara fitowa a fina-finai, tun da ‘yan film din ba amfanar al’umma suke yi da komai ba irinsa.

Ko a watannin baya, sai da jama’a suka turawa mawakin makudan kudade wanda ya ce zai buga musu waka, wakar da har yanzu ba ita ba labarinta.


Source link

Related Articles

7 Comments

  1. 581753 507549I really got into this article. I identified it to be intriguing and loaded with exclusive points of interest. I like to read material that makes me feel. Thank you for writing this wonderful content material. 851750

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news