Labarai

Maza sun koka kan yadda kasuwancin ‘Maniyyi’ ba ya kawo kudi masu daraja a Abuja

Wasu maza a babban birnin tarayya Abuja sun koka da yadda ba a samun kudi da yawa a harkan sitar da maniyi a Najeriya.

Mazan sun fadi ra’ayoyin su ne a a wani bincike da aka gudanar kan tasirin bada maniyi a kasar nan.

Kimiya ya fito da wannan tsari domin tallafawa ma’auratan da basu iya haihuwa.

Sai dai mazan Abuja sun ce kudin da ake siyan maniyi wajen mazaje bai taka kara ya karya ba.

Sannan ga yawan gwaje-gwaje da za a yi wa mutum domin tabbtar da ingancin maniyinsa.

A dalilin haka ne wani lauya Kalu Ekene ya ce shi ba zai iya bada maniyinsa ba saboda yadda abin ke neman zama aikin banza duk da cewa abin aiheri ne mutum ke yi.

“Ko da na je bada maniyi na sai da aka yi mun gwajin cututtuka da suka hada da kanjamau, hepatitis, cututtukan sanyi da dai sauran su.

“Bayan haka ne aka biya ni naira 150,000 wanda idan ka kwatanta yawan kudin da ake biyan mazan dake bada maniyinsu a kasashen waje ya fi haka yawa.

Ma’aikacin gwamnati Patrick Akpan ya ce abin da ya fi bata masa rai shine yadda ake yin sirri a harkan.

“Bayan wannan gwaje-gwajen da aka yi za kuma a ce ba a so kasan wanda zai yi amfani da maniyin ka ko ɗan da za a haifa da shi.

Shi kuwa bakaneke Yakubu Tobias cewa yayi bashi da matsala da ƙanƙanen kudin da ake biya amma yana da matsala da yadda suke tattance mutum kafin ya bada maniyinsa.

“Ni dana je sai da aka yi mu tambayoyi yadda kasan jarabawa na je rubutawa sannan bayan gwaje-gwajen da aka yi mun sai aka ce mun wai tsawo na bai kai yadda ake so ba.

Matsalolin dake tattare da bada maniyi a Najeriya

Likitan mata Isaac Shamaki ya ce tsarin bada maniyi tsari ne da kimiya ta kirkiro domin taimakawa wadanda ke bukatar haihuwa.

Tsarin iri biyu ne akwai wanda ma’aurata, wato mata da miji za su kawo wanda suke so su samu da da maniyinsa da Kuma wanda asibiti za su bada bayan sun tabbatar da ingancin maniyyin.

Shamaki ya ce tattance mutum da asibiti ke yi na taimakawa wajen samun ingantacen maniyin da zai iya haifar da ɗa.

Ya ce babban matsalar da ke tattare da bayar da maniyi shine tsufa domin da zarar namiji ya dara shekaru 39 maniyinsa ba shi da karfi da inganci sosai.

“Domin samun maniyin da zai oya zama ɗa ya kamata a samu daga wurin matashi domin shi maniyi ya kan ɗauki tsawon lokaci kafin ƙarfinsa ya kare.

Shamaki ya ce duk da cewa tsarin na taimakawa wajen samun haihuwa da inganta zaman aure wasu mazan da dama na da matsala wajen riƙe ɗa ta ciyar da ɗan dan da suka tabbatar ba nasu bane.

“Wannan na daga cikin matsalolin da ya fi ci mana tuwo a kwarya duk da lallashi da shawara da likita zai iya bai wa wasu masu bukatar yin aure.

Ya ce asibiti sun fi samun wannan matsala a wajen maza fiye da mata.


Source link

Related Articles

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button