Labarai

Mijina mugu ne ya kan tilasta ni yin azumi dole kuma Kasurgumin matsafi ne – Aisha a Kotu

Wata matar aure Aishat Zakaria ta kai karar mijinta Taofeek a kotun gargajiya dake Mapo a Ibadan domin kotun ta raba auren ta saboda cin zarafin ta da mijinta ke yi mata.

Aishat ta ce Taofeek mugun mutum ne domin ya kan tilasta yin azumi dole lokacin da take da ciki.

Ta Kuma ce Taofeek wanda ke sana’ar siyar da kayan gini na tsafi da shiga malamai.

“Taofeek kan lakada min dukan tsiya har na kan ji rauni a jikina.

Alkalin kotun Mrs S.M. Akintayo ta raba aurenganin yadda Aishat ta nuna alamun cewa akwai aure tsakanin ta da Taofeek.

Akintayo ta bai wa Aishat ikon kula da da ‘ya’ya biyu da suka haifa sannan shi Taofeek zai dauki nauyin biyan kudin makaranta, abinci da sauran bukatun yaran.


Source link

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *