Labarai

Minista Sadiya na so a kula da naƙasassun Najeriya kamar yadda ake yi a wasu ƙasashen

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Sadiya Umar Farouq, ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta samar wa da naƙasassun da ke Najeriya hanyoyin da za su riƙa bi a dukkan gine-gine da wurare na gwamnati irin su filayen jirgin sama, tashoshin jirgin ƙasa da na mota da makarantu.

Ministar ta yi kiran ne a lokacin da ta gabatar da Shugaba da membobi da Babban Sakataren Cibiyar Naƙasassu ta Ƙasa ga Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis a fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Sadiya ta gode wa Shugaban Ƙasa saboda yadda ya amsa kiran naƙasassun ta hanyar rattaba hannu kan Dokar Kula da Naƙasassu ta Ƙasa sannan ya kafa Hukumar Naƙasassu ta Ƙasa. Amma ta yi nuni da cewa mutane masu naƙasa a ƙasar nan an ware su daga cin moriyar wasu ababe na more rayuwa.

Ta ce sama da kashi 95 cikin ɗari na gine-ginen gwamnati da ke ƙasar nan ba su shiguwa a wajen naƙasassu sannan yawancin su su na buƙatar wasu na’urori da hanyoyin kimiyya da fasaha da za su taimake su wajen samun ilimi da koyo a cikin sauƙi.

Ta ce, “Akwai buƙatar a fito da hanyoyin da za su rage rainin da ake yi wa mutane masu naƙasa ta hanyar fito da babban gangamin faɗakar da jama’a, tare da cire duk wasu nau’o’i na nuna wariya da kuma inganta hanyoyin su na samun abinci.

“Akwai buƙatar a samu cikakkun bayanai game da naƙasassu, sannan bada satifiket ɗin naƙasassu ya na da muhimmanci wajen tabbatar da cewa su na cin moriyar wannan hukumar don a kauce wa cutar da wasu za su iya yi a aikin kyautatawar da gwamnati za ta riƙa yi.”

Har ila yau ministar ta bayyana cewa ta bai wa naƙasassu kayayyakin agaji don tabbatar da cewa su ma sun amfana da ayyukan da ma’aikatar ta ke yi da kuma dukkan shirye-shiryen inganta rayuwa.

Ta ce, “A yau dubban naƙasassu an taimaka masu kai-tsaye ta hanyar shirye-shiryen mu daban-daban.”

Sadiya ta yi kira ga gwamnati da ta ci gaba da bada goyon baya don tabbatar da cewa an kyautata rayuwar dukkan naƙasassu da ke Najeriya.

A jawabin da ya mayar, Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙalubalanci Hukumar Naƙasassu ta Ƙasa da ta yi aikin ta sosai wajen ganin an cimma ƙudirin gwamnati na ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga ƙangin fatara da yunwa.

Ya ce, “Ba a yi kuskure ba wajen naɗa ku da aka yi domin kuwa dukkan ku an zaɓo ku ne bayan an yi nazari sosai kan halayen ku da kuma gudunmawar da ku ke bayarwa ga al’umma da kuma naƙasassun da ke Nijeriya.

“Aikin da ke gaban ku babba ne. Tilas ne ku yi aiki tuƙuru domin tabbatar da cewa gwamnati ta samu nasarar inganta rayuwar ‘yan’uwan ku masu buƙatu na musamman duk da rashin isassun kuɗi da mu ke fama da shi.”

Shugaban ya bada tabbacin cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da bada goyon baya ga duk wasu yarjejeniyoyi da ke kare haƙƙin mutane masu naƙasa.

Ya ce, “Najeriya ta na cikin ƙasashen da su ka rattaba hannu kan Ƙudirin Majalisar Ɗinkin Duniya kan Mutane Masu Naƙasa wadda ke neman ganin an kare haƙƙin naƙasassu a dukkan wani shiri na kawo cigaba a duk duniya.

“A ƙarƙashin shugabanci na, gwamnati za ta ci gaba da goyon bayan duk wasu yarjejeniyoyi da aka yi na duniya da yanki ko sashen ƙasa da ƙasa waɗanda ke neman inganta rayuwar ‘yan’uwan mu masu buƙatu na musamman.”

Tun da fari dai sai da Majalisar Dattawa ta gama aikin tantance tare da amincewa da naɗin Hon. Dakta Husseini Hassan Kangiwa daga yankin Arewa Maso Yamma a matsayin Shugaban Hukumar Naƙasassu ta Ƙasa kamar yadda Sashe na 32(3) da na 40(1) na Dokar Hana Wariya Ga Naƙasassu ta 2019 ta tanadar.

Sauran membobin hukumar su ne:

Mrs. Esther Andrew Anwu,
Memba daga Arewa ta Tsakiya

Malam Abba Audu,
Memba daga Arewa ta Gabas

Malama Amina Rahma Audu,
Memba daga Arewa ta Yamma

Mista Jaja Oparaku,
Memba daga Kudu Maso Gabas

Ms. Philomena I Konwea,
Memba daga Kudu Maso Kudu

Mista Omopariola Busuyi,
Memba daga Kudu Maso Yamma

Mista James David Lalu,
Babban Sakatare, daga Arewa ta Tsakiya


Source link

Related Articles

35 Comments

 1. Good day! This is my 1st comment here so I just wanted to give a quick shout out and say I truly
  enjoy reading your blog posts. Can you suggest any other blogs/websites/forums that go over the same
  subjects? Thank you!

 2. When I originally commented I clicked the “Notify me when new comments are added” checkbox
  and now each time a comment is added I get four e-mails with the same comment.
  Is there any way you can remove me from that service?
  Thanks!

 3. Heya i’m for the primary time here. I came across this board
  and I to find It truly helpful & it helped me out much.
  I hope to give one thing back and aid others such as you aided me.

 4. [url=http://lasix.monster/]lasix price uk[/url] [url=http://tadalafilbrem.com/]tadalafil tablet buy online india[/url] [url=http://ivermectinxl.online/]price of stromectol[/url] [url=http://cialiszr.com/]cialis 10 mg tablet[/url] [url=http://ivermectinztab.online/]generic stromectol[/url]

 5. [url=http://trazodone.live/]trazodone brand name canada[/url] [url=http://atarax.live/]atarax 25 mg tablet price[/url] [url=http://cialiswise.com/]generic cialis 2018[/url] [url=http://amoxil.monster/]amoxicillin cost australia[/url] [url=http://tadlafil.com/]tadalafil pills online[/url] [url=http://vlviagra.com/]brand viagra for sale[/url] [url=http://100mgviagra.quest/]buy real viagra online cheap[/url] [url=http://synthroid.today/]synthroid 150 pill[/url] [url=http://chloroquinepills.quest/]online chloroquine[/url] [url=http://besttadalafilbuy.com/]tadalafil generic from canada[/url]

 6. [url=http://ivermectinztabs.com/]ivermectin online[/url] [url=http://viagravblue.com/]purchase cheap viagra[/url] [url=http://chloroquinepills.quest/]weimerquin[/url] [url=http://anafranil.quest/]anafranil cheap[/url] [url=http://medviagra.com/]viagra online paypal[/url] [url=http://aurogra.online/]aurogra 100 mg[/url] [url=http://tadalafillily.com/]tadalafil canada 5mg[/url] [url=http://ivermectinvtab.com/]stromectol without prescription[/url] [url=http://tadlafil.com/]tadalafil prescription price[/url] [url=http://cialisgm.com/]south africa cialis[/url]

 7. What’s Going down i’m new to this, I stumbled upon this I have discovered It positively useful
  and it has aided me out loads. I hope to contribute & assist
  other users like its helped me. Good job.

 8. Undeniably believe that that you said. Your favourite reason appeared
  to be at the internet the simplest thing to have in mind of.
  I say to you, I certainly get irked even as people think
  about issues that they just don’t realize about.
  You managed to hit the nail upon the top
  and also defined out the whole thing with no need
  side-effects , folks could take a signal.

  Will probably be back to get more. Thank you

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button