Labarai

MUGUN IRI: Birtaniya ta ce ba za ta bai wa tsagerun IPOB da MOSSOB mafakar siyasa ba

Gwamnatin Birtaniya ta bayyana cewa ba za ta bai wa duk wani tsageran ɗan ƙungiyar IPOB da MOSSOB masu tayar da ƙayar bayan neman kafa ƙasar Biafra su ɓalle daga Najeriya ba.

“Duk mutumin da ya aikata laifin take haƙƙin ɗan adam ba zai yiwu mu ba shi mafakar siyasa ba.”

Haka gwamnatin UK ta bayyana a cikin wani sabon daftarin ƙa’idojin zaman gudun hijira a ƙasar.

“Idan mutum ya san ya shiga ƙungiya ko ya aikata irin ɓarnar da IPOB da MOSSOB ko ma wata ƙungiyar da ke kiran kan ta Biafra mai tayar da hankali da amfani da muggan makamai wajen ƙoƙarin cimma manufofin ta, to ba ya cikin waɗanda aka amincewa su yi gudun hijira ko zaman sansanin gudun hijira a bisa ƙa’idar dokar gudun hijira ta duniya. Don haka ba za a bari su samu mafakar siyasa a Birtaniya ba.”

Sanarwar sabon tsarin na Birtaniya ta ce Gwamnantin Najeriya ta ayyana IPOB a matsayin ƙungiyar ‘yan ta’addar, har da duk wata ƙungiya mai kama da ita ko da ke ƙarƙashin ta, kamar ESN. Saboda su na afka wa jama’ar da ba su ji ba su gani ba su na kashe su a Najeriya.

Duk da cewa Gwamnatin Najeriya ba ta ayyana MOSSOB a matsayin ƙungiyar ta’addanci ba, amma bai ta na afka wa mutane da farmaki sosai.

Cikin wannan makon ne MOSSOB ta nemi Gwamnatin Najeriya ta saki Nnamdi Kanu, kuma a ba ƙabilar Igbo shugabancin ƙasa a 2023.

Kwana ɗaya kafin Shugaba Muhammadu Buhari ke shirin kai ziyara Jihar Ebonyi da ke Kudu maso Gabas a ranar Alhamis, a wata ziyarar kwana biyu, ƙungiyar MASSOB ta ƙabilar Igbo gurguzu sun nemi a gaggauta sakin Nnamdi Kanu daga tsare shi da ake yi.

Daga nan kuma sun nemi lallai a bai wa ƙabilar Igbo damar yin shugabancin Najeriya a 2023.

MASSOB ta yi wannan kakkausan bayani ne a cikin wata sanarwa da shugaban ta Uchenna Madu ya sa wa hannu kuma ya fitar a ranar Laraba.

Kanu dai shi ne Shugaban IPOB da ke tsare ana ci gaba da shari’ar sa a Abuja, tun bayan da jami’an tsaron Najeriya su ka sungumo shi daga Kenya, cikin 2021.

Ana tuhumar sa da cin amanar ƙasa da kuma ta’addanci.

MASSOB da IPOB dai Ɗanjuma ne da Ɗanjummai. Dukkan su na hanƙoron neman kafa ƙasar Biafra, ta gurguzun zallan ƙabilar Igbo. Wato neman ɓallewa daga Najeriya, ta hanyar tashe-tashen hankula.

Yayin da Shugaban MOSSOB ya ce ba ya jayayya da ziyarar da Buhari zai kai a Ebonyi, amma ya ce sakin Nnamdi Kanu zai rage yawan tashe-tashen hankula da kashe-kashen da ake yi a yankin.

“Yayin da Shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyarar kwana biyu a Ebonyi, ina tabbatarwa da kuma tunatar da Shugaban Ƙasa cewa sakin Nnamdi Kanu ne kaɗai zai kawo sauƙin tashe-tashen hankula a Kudu maso Gabas.

“MASSOB na kuma tunatar da Shugaba Muhammadu Buhari cewa ci gaba da tsare Kanu a hannun DSS zai ƙara tunzirawa da ruruta wutar fitintinun kawai. Kuma zai kara munana tattalin arziki a yankin.”

Sannan kuma ya ce a bai wa ƙabilar Igbo damar zama Shugaban Ƙasa zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin a zaɓen 2023.

Buhari zai kai ziyara Ebonyi domin buɗe wasu ayyukan da Gwamnan Jihar ya yi.


Source link

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button