Bidiyoyi

Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

Gwamnan jihar Kaduna kuma jigo a jam’iyyar APC, Nasir El-Rufai ya yi ikirarin cewa mutanen yankin Arewa mutane ne da suka san ya kamata. Ba za su yi wa wa ɗan takarar shugaban kasa na APC butulci ba.

El-Rufai wanda na daga cikin waɗanda suka yi jawabi a wurin taron ƙaddamar da Kamfen ɗin shugaban kasa na Jam’iyyar APC da aka yi a garin Jos ranar Talata ya ce Ƴan Arewa za su saka wa Tinubu bisa goyon bayan da ya baiwa Buhari a tsawon shekaru 8.

” Tinubu ya yi wa Arewa zumunci kuma ya nuna wa yankin da mutanen da mutanen yankin ƙauna da soyayya karara. Ya mara wa Buhari baya ya kuma tabbatar cewa Buhari ya samu goyon baya 100 bisa 100 a yankin kudu maso yamma da nan ne asalin sa.

” Yanzu lokaci yayi da muma za mu nuna masa ƙauna mu mara masa baya domin samun nasara a zaɓe mai zuwa.

Bayan haka El-Rufai ya gargaɗi mutanen Arewa da su toshe kunnuwar su kada su saurari mutanen dake yadawa wai Tinubu ba ya kishin Arewa.

” Ina so in tabbatar muku cewa a lokacin da Tinubu ke mulkin Legas ya ji da ƴan Arewa kuma ya basu dama sun yi kasuwancin su yadda ya kamata.

” Idan kuka bari PDP ta dawo toh za su dawo da yunwa ne, zasu tatike kasar kaf a koma gidan jiya.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button