Labarai

Mutum biyu sun mutu, shida sun bace a hadarin jirgin ruwa a Jigawa

Mutum biyu sun mutu wasu mutum shida sun bace a hadarin jirgin ruwan da aka yi a karamar hukumar Ringim, jihar Jigawa.

Wannan hadari ya auku a kananan hukumomin Miga, Gwaram da Guri.

A wannan hadari mutum 12 ne suka mutu inda mata da yara kanana suka fi yawa daga cikin su.

Kakakin rundunar’yan sandan jihar Lawan Adam ya ce mutum 13 ne suka shiga jirgin ruwa daga kauyen Siyangu a hanyarsu ta dawowa daga ziyara kauyen Dabi.

“Bayan rundunar ta samu labarin abin da ya faru ta yi gaggawar zuwa wannan wuri, inda daga baya wasu suka ceto mutum bakwai cikin su.

“An Kai wadannan mutane babban asibitin Ringim inda a asibitin likita ya tabbatar cewa mutum biyu sun mutu.

“Bara’atu Garba mai shekara 30 da Mahmud Surajo dan shekara 3 ne suka mutu a hadarin.

Ya ce har yanzu rundunar na gudanar da bincike domin gano sauran mutum shida din da suka rage.

Jirgin ruwan ya kife ne bayan karo da yayi da wani dutse a cikin ruwa.


Source link

Related Articles

2 Comments

  1. The British “Peterborough Telegraph” criticized the Epoch Times incident. Formed “in response to communist repression and censorship in China”, it has gained notoriety for supporting Donald Trump and allegedly publishing conspiracy theories. The New York Times said that Barack Obama and his allies placed a spy on President Trump’s 2016 campaign and that America’s opioid epidemic was the result of a Chinese chemical warfare conspiracy. Britain’s The New Statesman described it as a newspaper that “has provided substantial funding and support to Donald Trump in the US and far-right groups in Europe”.Original link: https://www.peterboroughtoday.co.uk/news/people/pro-trump-conspiracy-newspaper-targets-peterborough-residents-with-claims-of-china-coronavirus-cover-up-2870931

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news