Nishadi

NA GAJI DA JIRAN Pii YA FASHE: An ce Pii zai fashe, har yanzu shiru, na ga ji da narka Data na a yanar gizo – Garba

Wani magianci da ya daɗe ya harkar Pii wato diƙa shi ya na tara maki, ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa ya gaji da wannan barnan data da yake yi.

” Ni fa na daɗe ina mining Pii amma har yanzu abin shiru. Na gaji da gafara ga Sa nan amma ko kaho ba mu gani ba.

Abubakar magidanci ne wanda ya shaida mana cewa yana yin harkar Kirifto amma kuma daga baya ya tsinduma cikin harkar Pii. An ce man aidan Pii ta fashe ya mu zama miliniya.

” Ni fa an ce min idan Pii ya fashe zan iya siye layin mu a Kaduna, kuma an ce na yi sallama da talauci kenan. Amma kuma har yanzu bata fashe ba. Ko Datar da na ke yin amfani da shi ya kusa siyan babur irin roba-roba dinnan, wato (Wayyo Allah Kudina).

Abubakar da wasu da dama da suka tattauna da PREMIUM TIMES HAUSA a Kaduna sun ce daga yanzu za su fara ɗan daga kafa saboda hasarar ta yi yawa har yanzu babu riba.

Mutane da dama musamman matasa sun tsinduma cikin harkar Pii a yanar gizo, cewa idan ta fashe za su zama attajira. Sai dai kuma shiru har yanzu mutane ba su san halin da ake ciki ba.

Wasu dai har yanzu ba su cire tsammani ba cewa zata fashe kuma zasu kuɗan ce.


Source link

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *