Labarai

Na koma PDP ne don in kawo karshen mulkin kama karyar da APC ke yi a Jigawa – Saminu Turaki

Tsohon gwamnan jihar Jigawa Saminu Turaki ya sake komawa jam’iyyar PDP daga APC.

Turaki ya shaida wa manema labarai a Kano cewa ya koma jam’iyyar PDP ne domin ya ceto jihar Jigawa daga mulkin kama karyar da APC ke yi a jihar.

” A matsayina na shugaba, ba na koma PDP bane don neman mun’ƙami, nakoma domin muhaɗa hannu jam’iyyar ta yi nasara a zabukan 2023.

Shugaban jam’iyyar Babandi Gumel ya ce Turaki ya dawo PDP ne tare da dubban magoya bayan sa.

Ya ce tuni ɗan takaran da ke neman kujerar ta sanata Roni ya janye takarar sa ya bar wa Saminu Turaki.

Idan ba a manta ba Turaki ya koma jam’iyyar APC daga PDP inda daga baya ya sake sauya sheka zuwa jam’iyyar APC yqnzu kuma ya koma PDP.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news