Labarai

Na maida albashin da aka rika biya na lokacin da na yi murabus, kafin Buhari ya sake naɗa ni hadimin sa – Bashir Ahmad

Bisa wani zargi da jaridar Peoples’ Gazette ta buga cewa wai gwamnatin shugaba Muhammay Buhari ta rika jibga wa Bashir Ahmad miliyoyin naira bayan yayi murabus kafin a sake naɗa shi hadimin Buhari, Ahmad ya ce duk ya maida waɗannan kuɗaɗe.

PG ta buga labarin yadda gwamnatin Shugaba Buhari ta riƙa jibga wa Bashir Ahmad miliyoyin naira a matsayin albashin sa duk da ya ajiye aiki ya fantsama siyasa.

Bashir ya ajiye aiki kamar yadda shugaba Buhari ya umarci duk wani ma’aikacin sa da ke sha’awar ya shiga takara ya ajiye aiki.

Hakan ne ya sa shima Bashir Ahmad ya ajiye aikin nasa ya kuma garzaya Kano domin yin takarar ɗan majalisa Tarayya.

Bayan rashin nasara a zaɓen fidda gwani da yayi wanda ya yi zargin an yi masa murɗiya ne, Bashir ya dawo fadar shugaban kasa, inda a cikin makon jiya Shugaba Buhari ya nada shi mukamin mai taimaka masa na musamman.

Sai dai kuma takardar bitan albashi na wata wata da aka biya shi ya nuna an rika biyan Bashir albashin sa cif cif ko a lokacin da ya ajiye aikin tana karakainar takarar ɗan majalisa a Kano.

An biya Bashir sama da naira miliyan 3 cikin waɗanna watanni uku banda dimbin alawus alawus ɗin da zai rika karba a matsayin sa na hadimin Buhari.

Sai dai kuma PG ta ce Bashir ya bata amsar cewa ko da aka biya sa waɗannan kuɗade na watannin da baya aiki, ya maida wa gwamnti kudin cif. Amma kuma bai iya bada shaidar maida kuɗaɗen ba baya ga faɗi da yayi da fatan baki.


Source link

Related Articles

5 Comments

 1. Unquestionably believe that which you said. Your favorite justification appeared to be on the net the easiest
  thing to be aware of. I say to you, I definitely get annoyed while people think about worries that they plainly
  do not know about. You managed to hit the nail upon the
  top as well as defined out the whole thing without having side
  effect , people can take a signal. Will probably
  be back to get more. Thanks

 2. I’ve learn some just right stuff here. Definitely price bookmarking for revisiting.
  I surprise how much attempt you set to make one of these great informative web
  site.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news