Nishadi

Nafeesat ta yi bankwana da fim ‘Labarina’, ta ce ba za ta sake fitowa a shirin ba

Fitacciyar ƴar wasn fina-finan Hausa Nafeesat Abdullahi ta sanar wa masoyanta cewa ba za ta sake fitowa a shirin fim din Labarina na.

Labari wani fim ne mai dogon zango da yayi suna matuka a Arewacin Najeriya wanda Kamfanin Saira Movies ke haska.

Nafeesat da aka ke kira Sumayya a fim din Labarina ta ce ta yanke shawarar daina fitowa a shirin ne saboda ayyuka da suka yi mata yawa yanzu.

Nafeesat ta rubuta wasikar daina fitowa a shirin ne wanda ta aika wa mai shirya shirin Aminu Saira kuma ta ska a shafinta ta Instagram.

Ta ce ita ma tana sonbta fara nata finafinai sannan kuma ta na da harkokin kasuwancinta da kuma karatu da take yi.

” Wadannan suna suka sa ba zan iya ci gaba da fitowa a fim din Labarina ba.”

Karanta wasikar Nafeesat

Labarina Project ne da nake alfahari da shi ah duk inda na shiga. Saira Movies is also like my own company because mun Jima Muna aiki tare. I’m very sad to let you all know bazan ci gaba da Aikin Labarina ba, dalili shine rashin samun lokaci na yadda ya kamata, i have my own businesses, school, a company to run and also my own films that I’m planning to start shooting very soon. Bazan ce ah jira ni sai sanda na samu lokaci ba, dole za’a ci gaba da film din Labarina ko da ni ko ba ni.

Ina ba dubban masoya hakuri Akan fita ta daga shirin. Alakata da Saira movies Zata ci gaba da tafiya lafiya, babu hayaniya ko cin zarafi, Allah Kuma ya basu sa’a Wajen kammala sauran shirin.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button