Labarai

Nan da ƴan kwanaki kaɗan shafin Tiwita zai dawo aiki a Najeriya – Lai Mohammed

Ministan yaɗa labarai, Lai Mohammed ya bayyana cewa nan da kwanaki kaɗan masu zuwa, shafin Tiwita zai dawo da ci gaba da aiki a Najeriya.

Minista Lai ya bayyana haka ne a zantawa da manema labarai da yayi bayan taron majalisar Zartaswa ta Kasa da aka yi a fadar shugaban Kasa.

Lai ya ce ba za a ɗauki tsawon lokaci ba tiwita zai dawo aiki a Najeriya.

” Tattaunawar da muka yi da tiwita ya nuna lallai nan ba da dadewa ba zai dawo aiki a kasar nan.

Idan ba a manta ba, gwamnatin tarayya ta dakatar da Tiwita daga aiki a Najeriya tun a watan Yuni, saboda cin fuska da ya yi wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Kamfanoni da dama sun koka kan dakatar da tiwita ɗin da aka yi cewa hakan ya kawo musu cikas a ayyukan su.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button