Labarai

NDA ta ƙaryata wai an damke wani Sajen dake da hannu a harin da aka kai wa makarantar

Kakakin jami’ar NDA dake Kaduna Manjo Bashir Jajire ya karyata raɗeraɗin da kafafen yaɗa labarai suka buga wai an damke wani soja mai muƙamin Sajen mai suna Torsabo Solomon da ake zargi da hannu a harin da aka kaiwa makarantar a watan Agusta.

Idan ba a manta ba, an kai wa NDA hari a cikin Agusta, inda maharan da suk afka makaranta suka kashe wasolu sojoji biyu kuma suka sace wani Soja ɗaya, Stephen Dantong.

Maharan sun saki Stephen Dantong bayan kwashe makonni uku tsare a hannun su.

A takardar da Jajire ya fitar ranar Litinin, ya yi kira ga mutane da su yi watsi da wannan rahoto.

” Babu wani abu mai kama da haka da ya auku a. Solomon na nan babu abinda ya haɗa shi da harin da ƴan bindiga suka kai makarantar.

” Abinda muke so mutane su sani shine NDA ba wurin bincike bane makarantar horas da sojoji ne, saboda haka muna kira ga mutane su yi watsi da wannan labari da ake yaɗawa, babu wanda aka kama tukunna.

A ƙarshe Jajire ya ce nan ba da daɗewa ba za a kama waɗanda suka aikata wannan harin bazata a kuma hukunta su.

Jihar Kaduna kamar wasu jihohin Arewa Maso Yamma na fama da tsananin rashin tsaro musamman ayyukan ƴan bindiga da yaki ci yaki cinyewa.


Source link

Related Articles

11 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button