Labarai

NDLEA ta yi kamen masu harƙallar muggan kwayoyi, har da wanda ya kantara kashin kullin ‘KoKen’ 47

Hukumar Hana safara da tu’ammali da muggan Ƙwayoyi, NDLEA ta kama wani matashi dan shekara 26 mai suna Aloysius Onyekwe da kulin hodar ibilis guda 47.

Hukumar ta kama Onyekwe a Ibadan bayan ta samu bayanan siri game da harkallar kwayoyi da yake yi.

Darektan yada labarai na hukumar Femi Babafemi ya sanar da haka a Abuja.

Babafemi ya ce hukumar ta kama Onyekwe a hanyarsa ta zuwa kasar Algeria ta jihar Sokoto a mota.

Ya ce a lokacin kulin hodar ibilis din na cikin matashin inda bayan an kama shi ya yi bahayan su sau biyar.

“Onyekwe dan asalin karamar hukumar Owerri ta yamma ne a jihar Imo.

Hukumar ta kama shi a ranar 3 ga Yuly a Ojoo park za shi jihar Sokoto inda daga nan ya wuce zuwa kasar Algeria.

“Hukumar ta kama Onyekwe tare da wata matashiya Blessing Nwoke mai shekara 18.

Sannan kuma a jihar Oyo hukumar ta kama wani dillalin kwayoyi mai suna Mustapha Ijabula mai shekara 22 da kwayoyin tramadol 1,900.

Hukumar ta kama Ijabula a Yola jihar Adamawa yayin da hukumar ke caje mutane da motoci a kan hanyar Legas zuwa Ibadan.

NDLEA dake aiki a ruwa ta kama Fonkou Dassi mai shekara 31 da kwayoyin tramadol 6,000 ranar Juma’a.

Hukumar ta kama Dassi yayin da ya shiga jirgin ƙasa za shi kasar Kamaru.

Dassi ya boye kwayoyin tramadol a cikin kwalin indomine.

hukumar ta kama wani shahararren dillalin muggan kwayoyi mai suna Uduak Samuel mai shekara 29 ranar 5 ga Yuli a kotun da aka gurfanar da matarsa.

Samuel ya gudu ya bar tabar wiwi da ya kai nauyin kg 9.

Bayan haka, Hukumar ta kama wata dillaliyar muggan kwayoyi Beauty Dauda Mai shekara 27 a jihar Edo da muggan kwayoyi da suka hada da Meth, hodar ibilis na ruwa, tabar wiwi da garin hodar ibilis.

NDLEA ta kama Beauty a hanyar zuwa jihar Legas daga Benin City ranar 6 ga Yuli.


Source link

Related Articles

7 Comments

  1. I’m amazed, I have to admit. Rarely do I come across
    a blog that’s equally educative and interesting, and let me
    tell you, you’ve hit the nail on the head. The issue is something which not enough people are
    speaking intelligently about. I’m very happy I found this in my
    hunt for something regarding this.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button