Ciwon Lafiya

NIMONIYA: Rashin isassun kayan aiki a asibitoci na cikin matsalolin dake kisan yara a jihar Jigawa – Kungiya

Shugaban kungiya mai zaman kanta ‘Save the Children International Nigeria’ Mercy Gichuhi, ta bayyana cewa rashin isassun kayan aiki domin dakile yaduwar ciwon sanyi dake kama hakarkari, nimoniya na daga cikin matsalolin dake kisan yara kanana ‘yan ƙasa da shekara biyar a Najeriya.

Gichuhi ta fadi haka yayin da kungiyar tare da hadin gwiwar kingiyar ‘GlaxoSmithKline (GSK)’ suka raba wa wasu asibitocin jihar Jigawa kayan aikin kula da masu fama da cutar Nimoniya a garin Dutse.

A lissafe kayan da kungiyoyin suka raba zai kai na naira miliyan 20 domin taimakawa asibitocin jihar.

Ta ce sakamakon wani bincike da aka gudanar a shekarar 2020 a asibitoci 12 a kasar nan ya nuna cewa rashin ingantattun kayan aiki musamman na’urorin shakar iska na cikin matsalolin dake kisan yara kanana da suka kamu da nimomiya musamman ‘ya’yan talakawa a kasar nan.

Sannan sakamakon wani bincike da asusun UNICEF ta gudanar a Najeriya ya nuna cewa ciwon nimoniya ya kashe yara kanana ‘yan ƙasa da shekara biyar 162,000 a shekaran 2018.

Gichuhi ta ce a dalilin haka ya zama dole a tallafa wa asibitocin kasar nan domin ceto rayukan yara kanana.

Cutar Nimoniya

Ciwon sanyi da ke kama hakarkari, nimoniya akan kama shi ne ta hanyar shakar gurbataccen iska da kuma yawan shan kayan sanyi.

Cutar na daya daga cikin cututtuka biyar dake kisan yara kanana ‘yan kasa da shekara biyar a duniya.

Sakamakon binciken da jami’ar ‘John Hopkins’ ta yi ya nuna cewa nan da shekaru 10 masu zuwa Najeriya za ta iya rasa yara ‘ƴan kasa da shekaru biyar akalla miliyan biyu a dalilin kamuwa da cutar sanyi ‘Nimoniya’.

Bisa ga UNICEF kasashen Nigeria, India, Pakistan, the Jamhuriyan kasar Kongo da Ethiopia na cikin kasashen da cutar nimoniya ta yi wa katutu a duniya.


Source link

Related Articles

51 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button