Wasanni

Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, ya yi bajintar zura ƙwallaye uku a wani wasan sada zumuntar da tsoffin ɗaliban sakandare ta Baptist Boys High School da ke Abeokuta.

An shirya wasan ne a ranar Litinin, domin murnar cikar makarantar shekaru 100 da kafuwa.

An dai yi wasan me tsakanin tsoffin ɗalibai da su ka haɗa har da Obasanjo, mai shekaru 86 a duniya, da kuma tsoffin malaman makarantar.

Obasanjo na ci gaba da burge ‘yan Najeriya, ta wajen yadda yake yawan motsa jikin sa.

Cikin 2022 ya tuƙa Keke NAPEP ya na haya a cikin Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Sannan kuma a ƙarshen 2022 ɗin dai an nuno shi ya diro daga kan wani dandamalin taro, kuma babu abin da ya same shi.

Hakan da ya ke yawan yi duk da yawan shekarun sa, ya na jama’a na ƙara zargin wani ɗan takarar shugaban ƙasa cewa shekarun sa sun zarce yadda ya yi iƙirari, domin idan aka dube shi, za a ga Obasanjo ya fi shi ƙwarin jiki, kazar-kazar ƙoshin lafiya.


Source link

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *