Labarai

PDP a Taraba na cikin tsaka mai wuya bayan fatali da wata yarjejeniya tsakanin ta da shiyoyin jahar

A daren Lahadin nan ne babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ta ayyana tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar a matsayin wanda ya lashe zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar shugaban Najeriya.

Atiku ya lashe zaɓen ne bayan da ya samu ƙuri’a 371, inda ya kayar da gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike wanda ya zo na biyu da ƙuri’a 237.

Kafin fara zaɓen ne gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da tsohon fitaccen ma’aikacin banki Hayatu-Deen sun janye wa Atiku, tare da umartar magoya bayansu su zaɓi Atiku Abubakar.

Atiku Abubakar gogaggen dan siyasa ne da ya shafe shekaru da dama yana jan zaren. Hasalima yana daga cikin jiga-jigan mutanen da suka kafa jam’iyyar PDP.

An haifi Atiku Abubakar ranar 25 ga Nuwamban 1946 a Jihar Adamawa da ke Arewa Maso Gabas, kuma ya kasance jigon dan siyasa kuma hamshakin attajiri a Najeriya.

Tun bayan da Najeriya ta dawo mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999, Atiku Abubakar ya kasance mataimakin shugaban kasar Najeriya na 11, a mulkin Shugaba Olusegun Obasanjo a tsakanin 1999 zuwa 2007

Ya mallaki katafariyar Jami’ar ABTI, wato American University of Nigeria a Jiharsa ta Adamawa.

Kamfaninsa na hada-hadar man fetur, mai suna Intels Nigeria Limited na hada-hada a kasashen Afirka da suka hada da Angola da Equatorial Guinea da Gabon da Sao Tome and Principe.

Atiku Abubakar ya tsunduma harkokin sisaya a 1993, kuma yana cikin makusantan tsohon mataimakin shugaban kasa na mulkin soji, Janar Shehu Musa Yar’adua.

Ya shiga jam’iyyu daban-daban tun da ya shiga harkokin siyasa.

An zabi Atiku Abubakar a matsayin gwamnan gwamnan Jihar Adamawa a 1998, ko da yake daga bisani Cif Obasanjo ya zabe shi domin kasancewa mataimakinsa.

Daga wancan lokacin zuwa yanzu, wannan ne karo na uku da Atiku Abubakar ke tsayawa takarar shugaban kasa, ko da yake ya tsaya zaben fitar da gwani sau da dama.

A shekarar 2007, jam’iyyar Action Congress of Nigeria (ACN) ta tsayar da shi takara inda ya sha kaye a hannun dan takarar PDP, Umaru Musa Yar’adua.

Kazalika a shekarar 2019 ya fafata da Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC amma bai yi nasara ba.

Sai kuma yanzu da PDP ta saye tsayar da shi takara domin fafatawa a zaben shekarar 2023.


Source link

Related Articles

2 Comments

  1. This is the right site for anybody who wants to understand this topic.
    You know so much its almost hard to argue with you (not that I actually would want to…HaHa).

    You definitely put a new spin on a topic that has been written about for
    a long time. Great stuff, just great!

    Also visit my blog post; business ideas

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news