Labarai

PDP ce kaɗai za ta iya maida wa ‘yan Najeriya annuri a fuskokin su – Liyel Mike

Tsohon Gwamnan Jihar Cross Riba, Liyel Imoke, ya bayyana cewa matsawar ‘yan Na son sake ganin hasken annuri a fuskokin su, to su fito su zaɓi PDP a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Imoke ya yi wannan kira ga magoya bayan PDP na jihar sa da ƙasa baki ɗaya, a lokacin da ya ke jawabi wurin ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na Atiku Abubakar da Ifeanyi Okowa, a jihar.

Ya ce kowa shaida ne kuma ya ji a jikin sa, irin halin ƙuncin da ‘yan Nijeriya su ka shiga a shekaru bakwai na mulkin PDP.

Daga nan ya ce ya zama wajibi idan ‘yan ƙasar nan su na bukatar sake rayuwa cikin annashuwa da farin ciki, to su zaɓi PDP, tunda sun jaraba APC, amma ta ƙara jefa jama’a cikin halin ƙunci.

Imoke ya yi kira da a zaɓi PDP tun daga sama har ƙasa, domin hakan shi ne zai sa sabuwar gwamnatin da PDP za ta kafa, za ta yi karsashin da za ta samar da ayyukan raya ƙasa da kuma fitar da miliyoyin mutanen da su ka afka cikin ƙunci, talauci da rashin tsaro.

Tsohon gwamnan ya yi wannan bayani da kuma kira a daidai lokacin da Atiku ya ce a shirye ya ke ya yi sulhu da hasalallun gwamnonin PDP biyar, waɗanda har yanzu ba su goyi bayan takarar sa ba.

A ƙarshen makon da ya gabata ne dai Atiku ya ce ya na maraba da tayin sulhun da rundunar Wike ta nemi a yi.

Ɗan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin PDP, Atiku Abubakar, kuma tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, ya bayyana cewa ya na maraba lale da tayin neman yin sulhu da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike da magoya bayan sa su ka nema.

Atiku ya kuma nuna cewa ya amince da sasantawa da su Wike ɗin domin a kawo ƙarshen rikici da dambarwar da su ka dabaibaye PDP.

Ya ce yin hakan abu ne mai muhimmancin da zai ƙara haɗa kan ‘yan jam’iyya, sannan ya ƙara ƙarfafa PDP ƙwarai da gaske.

Atiku ya yi tsinkayen cewa tun da aka fara wannan dambarwa da Wike da ‘yan ɓangaren sa, bai taɓa rufe masu ƙofar shiga a sasanta ba.

Daga nan ya yi kira ga dukkan shugabannin jam’iyya da magoya bayan ta su kasance masu goyon bayan wannan ƙoƙarin sasanci.

Idan ba a manta ba, bayan ɓangaren Wike ya ziyarci Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi, sun shaida wa manema labarai cewa har yanzu ƙofar zama a sasanta tsakanin su da Atiku da PDP a buɗe ta.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Atiku mai suna Paul Ibe ya fitar, ya ce sasancin shi ne mafi alheri domin a ƙara wa jam’iyya ƙarfi, karsashi, sannan kuma a samu haɗin kai baki ɗaya.

Sannan kuma a wurin ne Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai ya nemi afuwar zafafa kalaman da ya yi kan Atiku, inda ya ce da ya zaɓi Bafulatani, gara ya mutu.


Source link

Related Articles

3 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button