Labarai

PDP ta kafa kwamitin tantance masu takarar mataimakin shugaban ƙasa

Jam’iyyar PDP ta kafa kwamitin mutum 12 da za su tantance masu takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

Sakataren Yaɗa Labarai na PDP na Ƙasa, Ɗebo Ologunagba ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar yau Laraba.

Ya ce za a fara zaman tantance su a ranar Alhamis, da ƙarfe 10 na safe.

Ana raɗe-raɗin cewa hankali ya fi karkata kan Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas, matsayin wanda za a ɗauka ya yi wa Atiku Abubakar mataimakin takara.

Sauran waɗanda ake tunanin naɗawa sun haɗa da Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta da kuma Gwamna Udom Emmanuel na Jihar Akwa Ibom.

Tsohon Minista Tom Ikimi ne Shugaban Kwamitin Tantancewa, yayin da Aƙulu Sani Indabawa ke Sakataren Kwamiti.

Wasu daga cikin mambobin har da Osita Chidoka, Idris Wada da sauran su.

A ranar Juma’a, 17 Ga Yuni ne INEC za ta rufe karɓar sunayen masu takarar mataimakin shugaban ƙasa.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda laluben mataimakin takarar Atiku ya hana jiga-jigan PDP barcin kwana bakwai.

Yayin da jam’iyyar PDP ta tsayar da Atiku Abubakar ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, zaɓen wanda zai yi masa takarar mataimaki ya hana manyan jam’iyyar barcin da ba za su samu damar rintsawa ba, sai nan da wasu kwanaki biyu masu zuwa.

Shugaban PDP Sanata Iyorchia Ayu, ya bayyana cewa nan da sa’o’i 48 PDP za ta bayyana sunan wanda zai yi wa Atiku Abubakar takarar mataimakin shugaban ƙasa.

Ayu ya bayyana haka ne yayin da za a shiga taron kwamitin fito da mataimakin takara na Atiku Abubakar a ranar Talata.

Kwamitin dai ya ƙunshi gwamnonin PDP masu ci a yanzu da kuma gwamnonin PDP da su ka sauka, amma ba su canja sheƙa ba.

Akwai kuma Mambobin Kwamitin Zartaswa na PDP da kuma Mambobin Kwamitin Gudanarwa na jam’iyyar.

PREMIUM TIMES Hausa ta bada labarin yadda aka sa Atiku ke ruwan ido, ya rasa wanda zai ɗauka mataimaki tsakanin Gwamna Nyesom Wike da Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta.

Haka kuma wannan jarida ta buga labarin cewa INEC ta ce za ta rufe rumbun tattara sunayen ‘yan takara a ranar 17 Ga Yuni da 15 Ga Yuli.

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta gargaɗi jam’iyyu cewa za ta rufe rumbun ta na intanet, wanda ta ke tattara sunayen ‘yan takarar zaɓukan 2023 a ranakun 17 Ga Yuni da kuma 15 Ga Yuli.

INEC ta ce za ta rufe karɓar sunayen ‘yan takarar masu zaɓen shugaban ƙasa, mataimaki, sanatoci da na tarayya a ranar 17 Ga Yuni, sai kuma sunayen ‘yan takarar gwamna da na mataimakin sa da kuma sunayen ‘yan takarar majalisar dokoki, waɗanda za a rufe a karɓar su a ranar 15 Ga Yuli.

Shugaban INEC Mahmood Yakubu ne ya yi wannan gargaɗin a lokacin da ya ke ganawa da Kwamishinonin Zaɓe na Tarayya, ranar Alhamis a Abuja.

Yakubu ya tunatar da su cewa an kammala zaɓukan fidda-gwanin dukkan jam’iyyun da za su shiga takarar zaɓen 2023 tun a ranar 9 Ga Yuni.

“INEC na buƙatar a damƙa mata sunayen ‘yan takarar shugaban ƙasa da mataimakin sa da na Sanatoci da Mambobin Tarayya daga ranar 10 Ga Yuni zuwa Juma’a 17 Ga Yuni.

“INEC na buƙatar sunayen ‘yan takarar gwamna da mataimaki da sunayen ‘yan majalisar dokoki daga ranar 1 Ga Yuli, zuwa 15 Ga Yuli.

“Za a loda sunayen ne a cikin rumbun tattara sunayen ‘yan takarar zaɓen 2023 na intanet, wato ‘portal’.”

Yakubu ya ce INEC na buƙatar jami’ai huɗu na daga cikin kowace jam’iyya 18 da za su yi takara su loda sunan ɗan takarar su a cikin rumbun tattara sunayen.

Yakubu ya ce tuni INEC ta damƙa wa kowace jam’iyya lambobin ɗan makullin da ake buɗe rumbun da su, domin su shiga su loda sunayen ‘yan takarar su.

“Mu na ƙara jaddada cewa sai sunayen ‘yan takarar da su ka yi nasarar lashe zaɓen fidda gwani bisa tsarin da Sashe na 84 na Dokar Zaɓe ta 2023 ne kaɗai za a loda sunayen su a cikin rumbun.”

Haka nan kuma PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa ana sa-toka-sa-katsi kan Gwamna Wike wajen ƙoƙarin fitar da ɗan takarar mataimakin Atiku Abubakar a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Yayin da masu goyon bayan Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas su na tsaya kai da fata cewa shi ya fi dacewa a ɗauka mataimakin shugaban ƙasa a takarar Atiku ta zaɓen 2023, wasu shugabannin jam’iyya kuwa na cewa sai dai a ɗauki Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa.

Naci da dagewar da jiga-jigan da ke goyon bayan Gwamna Nyesom Wike a matsayin wanda zai yi wa Atiku Abubakar mataimakin takara cewa sai dai a ɗauke shi, hakan ya kawo tsaikon ga Atiku wajen zaɓen wanda zai yi masa mataimaki a PDP.

Tun a ranar 29 Ga Mayu ne Atiku ya yi nasarar lashe zaɓen fidda gwani na PDP, inda Wike ne ya zo na biyu.

A ranar 17 Ga Yuni ne dai Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC za ta rufe karɓar sunayen ‘yan takarar muƙamai daban-daban a zaɓen 2023.

Okowa dai ya mara wa Atiku Abubakar baya a zaɓen fidda gwani, kuma a yankin Kudu maso Kudu ya ke, inda Wike shi ma ya fito.

Yayin da aka ce hankalin Atiku Abubakar ya fi kwantawa da Okowa, amma ya kasa zaɓen sa, saboda masu matsa wa Atiku lamba sun ce zai fi kyau ya ɗauki Wike, saboda ya fi shi ginannar rumfar siyasa a ƙasar nan, kuma ya fi Okowa ƙarfin aljihu.

Masu goyon bayan Wike sun nuna yadda ya riƙa ceto PDP idan ta afka cikin rikici da kuma yadda ya ke ɗaukar hidimomin jam’iyya a jihohin da ba PDP ke da gwamnati ba.

Masu adawa da Wike na cewa gaskiya wani irin gaɓotarin mutum ne, wanda ba zai dace a ce da shugabanci ba.

Sannan kuma sun ce idan har PDP ta yi nasarar kafa gwamnati, to Wike ba shi da kimtsuwa, zai riƙa tayar da daru da raba kan mulki a fadar shugaban ƙasa.

Majiyar da ke kusa da Atiku ta ce ya yi wa Wike alƙawarin zai naɗa shi Ministan Fetur idan PDP ta yi nasara. Idan ba ya so kuwa, to shi zai kawo sunan wanda ya ke so a naɗa ministan fetur ɗin.

Sai dai kuma masu goyon bayan Wike na cewa ba su son Minista Fetur a yanzu. Sun ce “ɗinyar makaho ta nuna aljihun sa. Mataimakin shugaban ƙasa su ke so a bai wa Wike, domin wannan muƙamin ake nema a yanzu, alƙawari kuwa ba tabbas ba ne a cika shi idan an ci zaɓe.” Cewar masu goyon bayan Wike.

Atiku ya gaba da Gwamnonin APC 13 sa’o’i kaɗan bayan an bayyana Bola Tinubu ne ya yi nasarar zaɓen fidda-gwanin APC.

Taron dai da Atiku ya yi da gwamnonin, sun daɗe su na tattauna batun wanda zai ɗauka ya yi masa mataimakin takara.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button