Labarai

PDPn Jihar Anambra ta ce Peter Obi bai masu bankwana ba lokacin lokacin da ya fice ya koma LP

Shugabannin PDP na Ƙaramar Hukumar Anaocha da ke Jihar Anambra, sun yi tir da Peter Obi, ɗan takarar jam’iyyar LP na shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

Obi, wanda haifaffen ƙauyen Agulu ne cikin ƙaramar hukumar, sun yi taroy ƙananan hukumomi 21 na jihar, inda aka tattauna yadda ɗan takarar PDP na zaɓen shugaban ƙasa, Atiku Abubakar zai samu nasara, shi da ɗan takarar mataimakin sa, Ifeanyi Okowa.

Sun bayyana Peter Obi da cewa ɗan takarar soshiyal midiya ne kawai ba ɗan takarar siyasa ba.

Sun ce ƙaramar hukumar da Peter Obi ya fito ba su san da wata LP ba, PDP kaɗai su ka sani.

Obi ya yi gwamnan Anambra tsakanin 2006 da 2014 a ƙarƙashin APGA.

Ya koma PDP watanni bakwai bayan ya miƙa masa mulkin jihar a hannun Willie Obiano, cikin 2014.

Obi ya nemi tsayawa takarar shugaban ƙasa a PDP, amma kwanaki kaɗan kafin zaɓen fidda gwani, ya fice daga PDP ya koma LP, tare da cewa a PDP akwai wasu take-take da jam’iyyar ke yi, waɗanda sun ci karo da manufofin sa.

Ya samu damar fitowa takarar shugaban ƙasa bayan LP ta ba shi dama, ta tsayar da shi.

Sai dai kuma manyan PDP na ƙaramar hukumar sa sun ce bai tuntuɓe su ba, kuma bai nemi shawarar su ba lokacin da zai fice daga PDP.


Source link

Related Articles

5 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button