Labarai

Peter Obi ya fice daga PDP

Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi ya bayyana ficewar sa daga jam’iyyar daga jam’iyyar PDP sannan kuma da janyewa daga dakarar shugaban kasa da yake yi.

A wasikar da ya aika wa shugaban jam’iyyar na jihar Anambra, Obi ya ce ya zama dole ya hakura da ci gaba da zama ɗan jam’iyyar PDP daga yanzu sabo lalacewa da tabarbarewar al’amura da kanannaɗe jam’iyyar.

Obi yace ” Tsakani na da Allah na ba da gudunmawar da zan baiwa jam’iyyar PDP don cigabanta da kasa baki ɗaya daidai gwargwardo.

” Yanzu ba zan iya ci gaba da zama cikin ta ba, saboda haka na hakura da ita na kama gaba na.

” Ina yi muku fatan Alkhairi, na gode matuka.

Idan ba a manta ba Peter Obi ne ɗan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2019, na jam’iyyar PDP ta re da Atiku Abubakar.

Ana raderadin cewa akwai yiwuwar Obi ya tsinduma jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button