Labarai

Raddin Hadiza Bala Ga Sanata Binta Garba

Dakatacciyar shugabar Hukumar NPA Hadiza Bala ta maida wa sanata Binta Garba martani bayan ta yi ikirarin cewa ita ce ta kulla tuggun da yayi sanadiyyar cireta da aka yi daga mambar kwamitin gudanarwar Hukumar Kula da Tashoshin jiragen Ruwan Najeriya, NPA.

Hadiza Bala ta ce tun farkon kasancewar ta kan shugabancin NPA babu wani abu da ta rika yin nuku-nukun sa. Ta ce a bayyane kuma a kan ka’ida ta rika gudanar da komai.

Ta bayyana hujjonin ta kamar haka:

1. Lokacin da masu binciken kudi su ka mika wa Kwamitin Kudi rahoto, wanda ita Binta ta na cikin kwamitin, ko ta nemi karin bayani a wuraren da ta yi zargin an yi dungu?

2. Idan ta nemi karin bayani, me ya faru?

3. Idan masu binciken sun yi mata karin bayanin tambayar da ta yi, me ya hana a matsayin ta na mamba ta ce ba ta yarda a fitar da rahoton ba, domin ta na ganin akwai dungu a cikin sa?

4. Me ya sa ba ta gabatar da rahoto ba na ta a matsayin ta na wadda aka rinjaya saura su ka amince da rahoton kwamitin?

5. Me ya sa Binta ba ta yi magana ba a lokacin, sai yanzu za ta fito ta na bilumbituwa?

6. “To Binta dai na da ‘yancin fadar ra’ayin da duk ta ga damar fitowa daga bakin ta, dangane da mu’amalar ta da ni a Hukumar NPA, lokacin ta na mambar Hukumar Gudanarwa.

7. Ina tunatar da Binta cewa duk wanda ya zubar da mutuncin sa, ya bari aka yi amfani da shi wajen cin mutuncin bayin Allah, to akwai ranar sakayyar abin da shuka ta na nan ta na jiran sa.” Inji Hadiza Bala.

Korafin Binta Garba

Sanata Binta Garba Masi ta yi ikirarin cewa dakatacciyar Shugabar Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa, Hadiza Bala ta tsoma hannayen ta cikin harkallar kudaden hukumar ta NPA.

Binta wacce ta yi sanata mai wakiltar Shiyyar Adamawa ta Arewa tsakanin 2015 zuwa 2019, ta ce an cire ta daga mamba ta Hukumar Gudanarwar Tashishin Jirage, NPA saboda ta zare idanu a kan wata harkalla da wasu akkaluman kudade da Hadiza Bala ta baddala ko ta damalmala.NPA saboda ta zare idanu a kan wata harkalla da wasu akkaluman kudade da Hadiza Bala ta baddala ko ta damalmala.

Ta yi wannan ikirari ne a Abuja, ranar Lahadi da ta gabata.

Sai dai kuma a raddin da Hadiza Bala ta mayar mata, ta bayyana Sanata Binta a matsayin makaryaciya, ‘yar sharri, kuma wadda ta kasa kawo hujjojin zargin da ta yi.

Hadiza ta ce maganganun shirme da kazafin da Binta ta yi mata, bilumbituwar surutai ne kawai babu hujja.

“Kalaman ta Binta ta yi a kai na surutai ne da su ka nuna dama tun farko ta shiga cikin hukumar gudanarwar NPA don ta dibga lalata a hukumar, ba don ta kawo ci gaba ba.” Inji Hadiza.

A sanarwar da Binta Garba ta bayar, ta ce, “na ga an baddala alkaluman kudade, na nusar kuma na yi tambayar dalilin yin hakan, amma aka yi biris da ni. Babu wanda ya ba ni amsa har yau din nan, har aka kitsa tuggun da aka cire ni daga mamba ta Hukumar Gudanarwar NPA.”

Binta ta zargi Hadiza da cire wasu mambobi ba tare da umarnin Ma’aikatar Harkokin Sufuri ba.

“An nada ni mamba ta Hukumar Gudanarwar NPA cikin watan Maris, 2020. Cikin Janairu 2021 aka cire ni da Sanata John Akpanudoedehe. Kuma Hadiza Bala Usman ce ta kitsa tuggun tsige mu.”

Binta ta ci gaba da cewa ta rika nuna damuwa dangane da yadda Hadiza Bala ke tafiyar da makudan kudaden NPA. Ta ce idan aka tafi a haka, to akwai badakala a gaba, kuma tabbas sai an cire Hadiza daga shugabancin NPA.

“Babban aiki na a Hukumar Gudanarwar NPA shi ne na rika bin diddigin kudaden da ke shiga da wadanda ke fita. Kuma saboda hakan Shugaban Kasa ya nada ni mamba. To na gano wani dungun baddala kudade. Na yi magana, na yi tambaya amma ba a ba ni amsa ba.”

Binta ta ce har Minista Amaechi ta tuntuba, amma maimakon Hadiza ta gyara kuma ta koma kan mikakkar hanya, sai ta karya dokar NPA, ta kitsa tuggun cire Binta daga Hukumar Gudanarwar NPA.


Source link

Related Articles

119 Comments

  1. Pingback: ivermectin de 6

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button