Ciwon Lafiya

RANAR BADA JINI TA DUNIYA: Dalilan da ya sa ake wahalar samun jini a asibitoci

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta yi kira ga gwamnatocin kasashen Afrika da ta tsaro hanyoyin da za su taimaka wajen inganta bada da samun jini a asibitocin Afrika.

Shugaban WHO reshen Afrika Matshidiso Moeti ta fadi haka ne a taron ranar bada jini ta duniya da aka yi ranar Talata.

Moeti ta ce rashin ware kudade, rashin isassun ma’aikata na daga cikin matsalolin dake hana samun jini a kasashen Afrika.

Ta ce rashin jini na cutar da lafiyar mutum miliyan 7 duk shekara a Afrika.

Moeti ta ce a Afrika bukatan katin jini ya fi yadda ake samun jini yawa.

“Matsalar da Afrika ke fama da shi shine yadda bukatan jini ya fi yadda mutane ke bada jini.

“Sannan bullowar cutar korona ya taimaka wajen hana mutane bada jininsu a Afrika.

Ta ce ya zama dole a tsaro matakai da za su taimaka wajen samar da jini a asibitocin Afrika.

Moeti ta ce wayar da kan mutane kan mahimmancin bada gudunmawar jini kyauta, hada hannun da malaman adini da sarakunan gargajiya domin ganin mutane sun ci gaba da bada kininsu kyauta sannan gwamnati ta ci gaba da ware isassun kudade domin ganin an ci gaba da tallafa wa lafiyan mutane na daga cikin matakan da gwamnati za ta iya dauka domin Samar da jini a asibitocin Afrika.

Ranar bada jini ta duniya.

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta kebe ranar 14 ga watan Yuni ta kowace shekara domin wayar da kan mutane mahimmancin bada jinin su kyauta sannan da yi wa mutanen dake bada jinin su kyauta.

WHO ta yin haka zai taimaka wajen ganin an ci gaba da samun jini domin inganta lafiyar mutane a Afrika.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button