Ciwon Lafiya

RANAR ZAZZABIN CIZON SAURO: Kungiya ta raba kayan gwajin cutar kyauta a sansanin ‘yan gudun hijira a Abuja

Yayin da duniya ke tunawa da zazzabin cizon sauro wata Kungiya mai zaman kanta ta raba kayan yin gwajin cutar kyauta a sansanonin ‘yan gudun hijira dake Abuja ranar Lahadi.

Shugaban kungiyar ‘Foundation (BSOF)’ Sam Otoboeze ya ce kungiyar ta yi haka ne domin ta taya gwamnatin tarayya yaki da zazzabin cizon sauro a kasar nan.

Otoboeze ya ce yin haka zai taimaka wajen samar da kula ga talakawa mazauna sansanin dake yawan fama da zazzabin cizon sauro.

Shugaban kamfanin ‘Biotechnologies’ Eddy Agbo ya ce kayan gwajin da aka raba na amfani da fitsarin mutumcwajrn gano kwayoyin zazzabin cizon sauro a jikin mutum.

“Ganin haka ya sa muka raba wadannan kayan gwajin saboda rashin ingantattun asibiti da wuraren yin gwaji a sansanonin.

Shugaban gidauniyar ‘Leader Joe 1808’ Joseph Onus ya yi kira ga asu ruwa da tsaki da su hada hannu da gwamnati wajen ganin bayan zazzabin cizon sauro.

Shugaban kungiyar ‘360° Childhood and Adult Learning Initiative (360° CAL-Initiative)’ Ikponmosa Success ya tsaftace muhalli, saka maganin sauro a dakin kwana da yin feshin magani domin kashe kwari na cikin hanyoyin guje wa kamuwa da cutar.

Shugaban asibitin dake sansanin ‘yan gudun hijira Isa Umar ya jinjina tallafin da kungiyar ta kawo musu a sansanin musamman yadda hakan zai rage yawan kashe kudi da mazauna sansanin ke Yi a asibitin.

Zazzabin cizon sauro

Zazzabin cizon sauro cuta ce da ake kamuwa da ita a dalilin cizon sauro.

Alamun ta sun hada da zazzabi, ciwon Kai, rashin iya cin abinci, ciwon gabobin jiki da sauran su.

Cutar na iya yin ajalin mutum Idan ba a gaggauta neman maganin ba.

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta fitar da rahoto a shekaran 2019 da ya nuna cewa mutum miliyan 229 ne suka kamu da cutar sannan cutar ta yi ajalin mutum 409,000 a kasashe 87 a duniya.

Rahotan ya kara nuna cewa kashi 94% na yawan mutanen dake kamuwa da cutar da yawan dake mutuwa a dalilin cutar a kasashen Afrika suke.

A Najeriya cutar ta zama annoba inda a shekara mutum miliyan 53 na kamuwa da cutar sannan cutar na yin ajalin mutum 81,640 a shekara.

Kasashen duniyan da har yanzu suke fama da yaduwar Zazzabin cizon sauro sun Fara sa ran rabuwa da cutar kwata-kwata saboda labarin hada maganin rigakafin cutar da suka ji.

WHO ta kebe ranar 25 ga Afrilu na kowani sheka domin tattauna hanyoyin dakile yaduwar cutar a duniya.


Source link

Related Articles

98 Comments

  1. 630284 902656whoah this blog is magnificent i love reading your posts. Maintain up the fantastic function! You know, lots of folks are seeking about for this info, you can assist them greatly. 355458

  2. 596876 752205Hmm is anyone else experiencing difficulties with the images on this weblog loading? Im trying to locate out if its a issue on my finish or if its the blog. Any responses would be greatly appreciated. 816563

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news