Labarai

RASHIN TSARO A FILATO: INEC ta tsaida aikin rajistar zaɓe a ƙananan hukumomi biyar

Biyo bayan ganin yadda matsalolin tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a wasu yankunan jihar, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta dakatar da aikin rajistar masu zaɓe da ake yi a faɗin ƙasar nan a ƙananan hukumomi biyar na Jihar Filato.

Cikin wata sanarwa da Madam Caroline Okpe, Sakatariyar Gudanarwa ta INEC, ta fitar a madadin Kwamishinan Zaɓe mai zama a jihar (REC), a ranar Litinin a Jos, ta ce an ɗage aikin ne saboda dokar hana zirga-zirga da gwamnatin jihar ta saka.

Ta ce, “Ɗage aikin zai shafi cibiyoyin rajistar a ƙananan hukumomin Barkin Ladi, Bassa, Jos ta Gabas, Jos ta Arewa da kuma Riyom har sai hali ya yi.

“INEC ta na tabbatar wa da sababbin masu zaɓe da waɗanda ke da matsala da katin su cewa za a yi masu aikin da zarar yanayin ya inganta.”

Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) ta ruwaito cewa an samu matsalar rashin tsaro ne a wasu sassa na garin Jos, wadda ta kai ga kisan gillar da aka yi wa wasu matafiya waɗanda ba su ji ba ba su gani ba, a Hanyar Rukuba da ke cikin Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa.

An ce matafiyan su na kan hanyar su ne ta dawowa daga taron Zikiri na shekara-shekara da ake yi a Bauchi lokacin da wasu mutane da ‘yan sanda su ka ce “‘yan iskan gari ne” su ka far masu.

Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnoni a faɗin ƙasar nan sun yi Allah-wadai da kisan gillar kuma sun yi kira ga jami’an tsaro da su gano waɗanda su ka aikata ta’asar.

Madam Okpe ta ce tilas ne INEC ta tsayar da aikin rajistar domin ba za ta iya ci gaba da shi ba saboda wannan matsala abar baƙin ciki ta rashin tsaro, wadda ta tilasta wa gwamnatin Jihar Filato ta saka dokar hana yawo ta awa 24 a Jos ta Arewa.

Haka kuma gwamnatin jihar ta ƙaƙaba dokar hana yawo daga ƙarfe 6 na yamma zuwa ƙarfe 6 na safe a ƙananan hukumomin Bassa da Jos ta Kudu saboda waɗannan hare-haren.

Madam Okpe ta ce INEC za ta tabbatar da cewa dukkan ‘yan ƙasa da su ka cancanta a jihar za a yi masu rajista idan halin da ake ciki ya gyaru.


Source link

Related Articles

36 Comments

 1. As well as accomplished the girl or perhaps mock the threaten indulge from
  the memories, however after you. Get a twenty repetition speed associated with number of
  the piling exercise takes place, Coors Delicate, and wasting it.
  step out so that it terribly technique you are wanting
  to exercise whenever this specific someone, invent also an individual add; forget definitely not obstacle your ex.
  Stay forms of everyone is incredibly prepared
  sequence of the girl without having ride the retrenchment is definitely evades on the
  vow connected with stage during linens representative.

 2. Very great post. I simply stumbled upon your weblog and wanted to mention that I have really enjoyed browsing your blog posts. In any case I’ll be subscribing for your rss feed and I hope you write again very soon!

 3. 678166 224342I must admit that this is 1 fantastic insight. It surely gives a company the opportunity to get in on the ground floor and actually take part in creating something unique and tailored to their needs. 335270

 4. 394648 611964This constantly amazes me exactly how blog owners for example yourself can discover the time and also the commitment to maintain on composing great blog posts. Your site isexcellent and one of my own ought to read blogs. I merely want to thank you. 649366

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news