Labarai

RASHIN TSARO A KATSINA: Kananan Hukumomin da ke neman komawa hannun ’yan bindiga

Bayan garkuwa da dalibai 343 da aka yi a makonni biyu a Katsina, a ranar da aka damka su a hannun iyayen su kuma an yi garkuwa da daliban Islamiyya 80 a Karamar Hukumar Dandume cikin Jihar Katsina.

Idan ba a manta ba, cikin shekarar da ta gabata an yi garkuwa da mutum 73 a garin Wurma cikin Jihar Katsina.

Yayin da garkuwa da mutane ta zama ruwan dare mai sauka a kullum a Katsina, za a iya cewa kusan babu karamar hukumar da wannan mummunan lamari bai shafa ba.

Sai dai kuma abin ya fi muni a wasu kananan hukumomi da ke da kusanci da Jihar Zamfara da kuma Dajin Rugu.

Kananan Hukumomin da garkuwa da mutane ta fi yin katutu, sun hada da Sabuwa, Danmusa, Dandume, Faskari, Funtua, Kankara, Safana, Danmusa, Batsari, Jibiya, Kurfi da kuma Dutsinma.

Wannan ba ya na nufin duk sauran kananan hukumomin Katsina zaune su ke lafiya kalau ba. Kananan Hukumomi irin su Charanci ma na fama da masu shiga su yi takakkiya su saci mutum su nausa daji mai nisa da shi.

Kada a manta kuma har cikin garin Daura an je an sace Musa Daura, surikin Babban Dogarin Shugaba Muhammadu Buhari, wanda bayan dogon lokaci aka gano shi a wani gidan da aka boye shi a cikin Kano.

Cikin 2019 idan ba a manta ba, mun kawo rahoton yadda aka jera kwanaki 61 a kullum sai an yi garkuwa da mutum a Dutsinma, cikin Jihar Katsina.

Tsoron yadda ake shiga garuruwa ana farautar mai rufin asiri ko mai hasken kyawon gida, ya sa tuni Katinawa mazauna Kano da dama na dauko iyayen su daga cikin kauyuka su na maida su Kano.

Wasu kuma musamman ma’aikatan gwamnati da sauran masu hada-hadar rufin asiri, su na tashi cancak daga cikin garuruwan su tare da iyalan su, su koma cikin birnin Katsina.

Ta kai ta kawo a wasu kauyuka duk jarin masu kananan sana’o’i ya karye. Mutane da dama sun a sayar da kadarori musamman gonaki su na biyan diyyar fansar rayukan dangin su da ke hannun masu garkuwa.

Wata kwakwarar majiya ta shaida wa wakilin mu cewa, “Yanzu haka wani da ka sani sun hakura da ‘yar su mai shekara 10 da aka yi garkuwa da ita.

“Sun nemi a kai kudin fansa, amma kakannin yarinyar ba su da komai, ba su da abin da za su sayar su karbo fansar yarinya.

“Kwanan nan sun buyo waya su ka ce yarinyar ta ishe su da kuka. Idan ba a je an karbo ta ba, to za su sake ta a cikin daji.

“Nan mahaifiyar yarinyar ta ce ita dai ta hakura, ta sallama kawai.”

Wani bincike da PREMIUM TIMES Hausa ta yi, ya tabbatar da cewa babu ranar da ba za a saci mutum a yi garkuwa da shi a jihar Katsina.

“Ko ita waccan yarinyar da aka sace, ai don sun san ta na da wani dan uwa a Kano ne su ka dauke ta. Sun dauka ya na da kudin da zai biya a fanso ta. Amma yanzu haka a kauyen kusa da garin mu ma wani mutum na cqn a tsare, har yau ana ta cinikin adadin kudaden da su ke bukata a biya, sannan su sako shi.

Haka kuma wata majiya ta tabbatar wa wakilin mu cewa wasu garuruwan Katsina jama’a na ta tanadar bindigogin kare kan su.

“Ka ga dai ‘yan sanda ba su iya kare kowa a garin nan. Ina tabbatar maka a hedikwatar karamar hukumar mu, ba za ka rasa mutum 500 da kowa ya tanadi bindigar gargajiya ta kare kan sa ba.”

Yadda mahara sun arce da ango da amarya, bayan sun kashe kawun dan majalisa

“Duk fa wannan rashin mutunci da rashin tausayin da aka tafka, akwai jami’an tsaro a kusa da inda ‘yn bindigar su ka kashe kawu na.” Haka Dan Majalisa ya shaida wa PREMIUM TIMES.

Wannan kisa da garkuwa sun faru ne a yankin Runka, cikin Karamar Hukumar Safana a Jihar Katsina, inda mahara su ka arce da amarya da ango, bayan sun bindige kawun Dan Majalisar Jihar Katsina, mai wakiltar Karamar Hukumar Safana.

Mazuna yankin sun shaida cewa abin ya faru a cikin Runka, inda mahara su ka kashe Sama’ila Supa, wanda kawu ne da Abdullahi Haruna, Dan Majalisa mai wakiltar Safana, a Jihar Katsina.

Da ya ke zantawa da PREMIUM TIMES, Honorabul Haruna ya ce an bindige kawun sa ya mutu bayan ya ki yarda a tafi da shi.

“Duk fa wannan rashin mutunci da rashin tausayin da aka tafka, akwai jami’an tsaro a kusa da inda ‘yan bindigar su ka kashe kawu na.” Haka Dan Majalisa ya shaida wa PREMIUM TIMES.

Ya ce tsakanin wurin da aka kashe kawun sa da inda jami’an tsaro su ke, bai wuce kilomita biyar ba, amma haka a kullum a yankin na su masu gakuwa ke shigowa su yi rashin mutunci, ku kama wanda su ka ga dama, su shiga daji da shi.

“Babu ranar da masu garkuwa ba za su shiga yankin mu su yi garkuwa da mutnae ba. Ko jiya da dare ma sun shiga garin Babban Duhu, su ka arce da mutum 13, amma daga baya bakwai su ka tsere da kyar, su ka kubuta. Sun kuma harbi mutane da dama, wadanda yanzu haka duk su na asibiti a kwance, ana kula da su.”

Limamin Masallacin Izala na Runka, Malam Yakubu, bayan ya yi wa gawa sallah, ya roki shugabanni su ji tsoron Allah, su tashi tsaye su kare rayuka da dukiyoyin talakawn su.

Sannan kuma ya ce ya kamata kowa ya tashi ya kare kan sa, domin a same ka a kashe, har gar aka mutu wajen kare kan ka.

Ita kuma amarya da angon ta da aka gudu da su, an sace su ne ranar Litinin, mako daya kacal da daura masu aure.

An bayyana sunan angon Sama’ila Abdullahi, ita kuma amaryar Zainab Isma’il.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa jami’ai na bakin kokarin su domin su kubutar da wadanda aka yi garkuwar da su.

Ya yi kira ga mazauna yankin su rika fallasawa da kai rahoton masu yi wamahara leken asiri, da ba su labarin wadanda za a yi garkuwa da su a samu kudi.

Har yau da I masu garkuwar bas u kira kowa ba, ballantana a ji abin da su ke so a biya su.


Source link

Related Articles

121 Comments

  1. 521305 559269I was recommended this web site by my cousin. Im not confident whether this post is written by him as nobody else know such detailed about my trouble. You are wonderful! Thanks! 363508

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news