KannyWood

Rasuwar Ahmad Tage asara ce ga Kannywood, inji MOPPAN da ‘yan fim

HAƊAƊƊIYAR ƙungiyar masu shirya finafinai ta Kannywood, wato MOPPAN, ta bayyana rasuwar ɗaya daga cikin dattawan masana’antar, Malam Ahmad Aliyu Tage, da cewa babban rashi ne.

Shugaban MOPPAN na ƙasa, Dakta Ahmad Sarari, shi ne ya bayyana haka jim kaɗan da rasuwar Tage, wanda fitaccen mai ɗaukar hoton bidiyo ne (cameraman) tun farkon kafa masana’antar.

Tage ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase, wanda aka fi sani Asibitin Nasarwa, da ke Kano, ɗazun nan.

Wata majiya ta faɗa wa mujallar Fim cewa ya rasu ne bayan ya samu matsalar bugun zuciya.

Shugaban ƙungiyar jaruman Kannywood, Malam Alhassan Kwalle, ya bada sanarwar cewa za a yi jana’izar mamacin anjima da ƙarfe 4:00 a gidan sa da ke unguwar Sheka Ƙarshen Kwalta.

Wannan mutuwa dai ta girgiza masana’antar ta shirya finafinan Hausa. Ɗimbin ‘yan fim su na ci gaba da yi wa Tage addu’ar samun rahama a shafukan su na soshiyal midiya.

Shugaban MOPPAN, Dakta Sarari, ya ce: “Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un! Hakika Kannywood ta yi babban rashi.

“Allah ya jiƙan Ahmad Tage. Allah ya yi masa rahama. Allah ya duba masa bayan sa, mu kuma in tamu ta zo Allah ya sa mu cika da imani.”

Shi ma tsohon shugaban MOPPAN na ƙasa kuma fitaccen jarumi, Alhaji Sani Mu’azu, ya ce mutane da dama za su ji wannan mutuwa da aka yi.

Ya ce ya na fatan ba za a taɓa mantawa da kyakkyawar rayuwar Tage ba da kuma gudunmawar da ya bayar ga cigaban Kannywood.

“Allah ya sa rashi da mu ke samu ya dinga zama wa’azi ga tamu rayuwar,” inji Sani Mu’azu.

Ɗaya daga cikin yaran marigayin, wato Ayatullahi Uba, wanda aka fi sani da Ayatullahi Tage, ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa maigidan nasa.

Ayatullahi, wanda shi ne shugaban kamfanin Tage Entertainment, ya faɗa a cikin alhini: “Allah ya gafarta maka. Allah ya sa ƙarshen wahalar kenan. Allah ya sa ka na cikin ‘yantattun bayin da Annabi Muhammad s.a.w. zai karɓi baƙuncin su.

“Allah ya jiƙan ka Baba; ka maye gurbin mahaifi a gare ni. Yau ce rana mafi muni a tare da ni. Allah ya gafarta maka. Allah ya sa ka huta, amin.”

To amin ya Allah.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button