Ciwon Lafiya

RIGAKAFIN KORONA: Sultan hori gwamnati ta fadada kamfen din wayar da kan mutanen Kasar nan

Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III ya yi kira ga gwamnatin da ta fadada kamfen din wayar da kan mutane game da allurar rigakafin cutar korona da za a shigo da su a watan Faburairu.

Sa’ad ya ce yin haka zai taimaka wajen kawar da rudanin da rashin yarda a tsakanin mutane wanda shine yanzu ya karade gari.

Ya fadi haka a taron wayar da kan malamai da limaman kasar nan game da maganin rigakafin Korona da hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na ƙasa NPHCDA ta shirya ranar Laraba.

Sultan ya kara da cewa lallai fa yana kira ga gwamnati ta maida hankali wajen wayar da kan mutane domin a gari rudani ake yadawa cewa wai maganin an kirkiro shi domin a kashe mutanen Afrika.

“Mutane na yada labaran cewa rigakafin korona gubace kuma anyi ta ne don a kashe mutane Afrika. Amma kada mu manta cewa tun ba yau ake shigo da magunguna daga kasashen waje sannan idan ma ana so a kashe mu din ne ai akwai hanyoyi da dama da za a iya bi ba sai ta rigakafin Korona ba.

“Yin allurar rigakafin korona kyauta ne amma amincewa da yin allurar ya rage ga mutanen kasa.

Yayin da cutar ke ci gaba da yaduwa kasashen duniya na kokawar samun maganin rigakafin cutar domin samar wa mutanen su kariya.

Duk da haka kasashen duniya na kokarin wayar da kan mutanen su domin amincewa da yin allurar rigakafin.

Ministan lafiya Osagie Ehanire ya ce Najeriya za ta karbi kwalaban maganin rigakafin gida 100,000 a watan Faburairu.

Bayan haka ministan ya kuma ce kamfanin Gavi ta bai wa Najeriya gudunmawar kwalaban maganin guda miliyan 42.

Ya ce duk wadannan maganin zai Isa a yi wa kashi 20% ne rigakafin cutar a kasar nan.

Ehanire ya ce gwamnati ta ware kudade domin siyo miliyan 10 na kwalaben maganin rigakafin.

Domin karkato da hankulan mutane kan amincewa da yin rigakafin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo ta gwamnonin Najeriya sun amince da su yi allurar rigakafin a talabijin domin kowa da kowa ya gani.


Source link

Related Articles

127 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news