Ciwon Lafiya

Rigakafin Korona zai iso Najeriya ranar Talata – Boss Mustapha

Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa Kan dakile yaduwar Korona ta Kasa, Boss Mustapha ya bayyana cewa Najeriya za ta karbi rigakafin maganin Korona akalla miliyan 4 ranar Talata.

” Idan dai ba an samu wani tangarda ko jinkiri ba ne jirgin rigakafin zai ta so daga Indiya ranar Litini ya iso Najeriya ranar Talata.

Muna sa ran daga wannan shekara zuwa 2022, za mu yi wa ‘yan Najeriya miliyan 70 rigakafin cutar Korona.

Korona a Najeriya

A ranar Lahadi ne aka samu mafi Karancin yawan wadanda suka kamu da Korona a Najeriya tun bayan barkewar cutar a karo ta biyu a Najeriya.

A cikin kwanaki 7 da suka wuce Najeriya ta samu karin mutane kasa da 700 da suka kamu da Korona. Mutum 341 ne suka kamu ranar Asabar.

Mutum 3 ne kacal suka mutu. Hakan ya nuna raguwa daga mutum 11 da suka rasu ranar Juma’a.

Hukumar NCDC ta bayyana cewa mutum 133,256 sun warke daga cutar cikin mutum 155,417 suka kamu a Najeriya.

An yi wa mutum 1,489,103 gwaji a kasar nan cikin ‘yan Najeriya akalla miliyan 200.

Yawan mutanen da suka kamu a jihohin kasar nan ranar Asabar

Lagos (96), Rivers (41), Kaduna (33), Edo (21), Osun (20), Akwa Ibom (17), FCT (17), Ondo (15), Gombe (11), Kano (11), Imo (10), Ekiti (9), Kebbi (9), Kwara (8), Oyo (8), Borno (6), Enugu (3), Plateau (3), Delta (1), Niger (1) and Ogun (1).


Source link

Related Articles

220 Comments

  1. Pingback: free 3d sex games
  2. Pingback: online casino
  3. Pingback: keto bhb reviews
  4. Pingback: keto candy
  5. Pingback: write a essay
  6. Pingback: gay tx dating
  7. Pingback: 200 word essay
  8. Pingback: poverty essay
  9. Pingback: narrative essay
  10. Pingback: 1boudoir

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button