Labarai

RIKICIN PDP: Duk mai jayayya da shugabancin Ayu ya fice kawai ya huta

Ɗan takarar gwamnan Jihar Ogun na jam’iyyar PDP, Ladi Adebutu, ya shawarci duk wani wanda bai yarda da shugabancin Iyorchia Ayu a matsayin Shugaban PDP na Ƙasa ba, to ya fice daga jam’iyyar kawai a daina ka-ce-na-ce.

“Kotun Ƙoli ta sha yin irin wannan hukunci. Idan ba ka gamsu da abin da ke cikin jam’iyyar da ka ke ciki ba, to ko dai ka haƙura a tafi a haka, ko ka fice daga jam’iyyar, ko kuma kai ma ka je ku kafa ta ku jam’iyyar.” Haka Adebutu ya bayar da shawara.

Ɗan takarar ya yi wannan kira ne, tare da nuna goyon bayan sa ga Ayu, a lokacin da shugabannin ƙabilu mazauna jihar Ogun su ka kai masa ziyara.

“Saboda haka Ayu shi ne shugaban jam’iyyar mu ta PDP, mu na goyon bayan sa, ba mu tare da masu son wai tilas sai an cire shi za su tafi tare da mu.

“Kuma nan a Jihar Ogun, mun yarda Honorabul Sikiralahi ne shugaban mu, shi ne kuma wakilin Ayu a jihar mu.

Adebutu ya na magana ne kan botsarewar da wasu gwamnoni biyar su ka yi, bisa jagorancin Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas, masu neman tilas sai Ayu ya sauka a naɗa wa PDP shugaba daga Kudu.

Daga cikin shugabannin ƙabilun da su ka kai masa ziyarar a ranar Asabar, akwai Hausawa, Igbo, Ijaw, Idoma da sauran su.

Tuni dai wannan dambarwa ta neman cire Ayu ta haifar wa PDP matsalar da har ta fara kamfen ba tare da goyon bayan gwamnonin biyar ba.

PDP Ba Za Ta Iya Cin Zaɓe Ba Tare Da Mu Gwamnoni Biyar Masu Neman A Yi Adalci Ba -Gwamna Wike:

Cikin tsakiyar Oktoba ne Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ya bugi ƙirjin cewa idan ba su bayar da goyon baya ba, to babu yadda za a yi jam”iyyar PDP ta yi nasarar zaɓen shugaban ƙasa a 2023.

Wike ya bayyana haka a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a Fatakwal.

Ya ce gwamnonin biyar da su ka haɗa da shi kansa, Ikpeazu na Abiya da su Ortom na Benuwai da Seyi Makinde na Ogun da Ifeanyi Ugwuanyi ba abin rainawa ba ne, kuma ba ƙashin jefarwa ba ne.

“Idan ba mu bayar da haɗin kai ba, to PDP kamfen ɗin banza ta ke yi, ba cin zaɓe za ta yi ba. Ko mazaɓar kansila ba za ta iya ci ba.”

Ya ci gaba da cewa masu maular ‘kudaden kama haya’ a hannun Ayu ke hana sasanta rikicin PDP.

Gwamna Nyesom Wike ya bayyana cewa wasu manyan ‘yan maular kuɗaɗen haya daga PDP ne ke hana ƙoƙarin da shi Wike ɗin ke yi domin a ɗinke ɓarakar da ke cikin jam’iyyar a cikin ruwan sanyi.

Wike da wasu gwamnonin PDP huɗu dai su na so Shugaban PDP Iyorchia Ayu ya sauka, a zaɓi ɗan kudu ya riƙe shugabancin jam’iyyar.

Wike ya yi zargin masu hana ruwa gudu a PDP ɗin, lokacin da ɗan takarar gwamnan Jihar Kuros Riba na PDP, Sandy Onor ya kai masa ziyara tare da wasu magoya bayan jam’iyyar.

Wike ya ce rikicin PDP ya ƙara muni ne haka kawai, saboda wasu marasa kishin jam”iyya da ya kira “kuraye da masu maular kuɗaɗen kama haya,” sun ƙi bari a wanzar da gaskiya, adalci da daidaito a cikin PDP.

Ya ce ba zai taɓa goyon bayan tafiyar PDP a yanzu ba, inda shugaban jam’iyya daga Arewa, ɗan takarar shugaban ƙasa daga Arewa sannan kuma Darakta Janar na Kamfen shi ma daga Arewa.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button