Labarai

RIKICIN PDP: Majalisar Zartaswar PDP ta goyi bayan shugabancin Ayu

Da alamu dai babu ranar warware rikicin PDP, yayin da Majalisar Zartaswar jam’iyyar (NEC) ta rattaba amincewa da shugabancin Iyorchia Ayu da sauran masu riƙe da shugabancin jam’iyyar (NWC) a ƙarƙashin Ayu.

Amincewar da su ya ƙara tabbata a taron manyan jam’iyyar da aka gudanar ranar Alhamis a Abuja.

Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Tarayya Ndudi Elumelu ne ya nemi a amince da su, kuma nan take aka amince.

Elumelu ya ce Ayu ya cancanci ya ci gaba da shugabancin PDP, ganin yadda ya jajirce aka yi nasara a zaɓen gwamnan Jihar Osun a ranar 18 Ga Yuli.

Ya kuma jinjina wa sauran mambobin NWC saboda dattakon da su ka nuna duk kuwa da rashin jituwar da ke tsakanin wasu mambobin na NWC.

Elumelu ya ce, “Ayu ya yi ƙoƙari, kuma idan aka bar shi ya ci gaba, shi da sauran shugabannin za su sa PDP ta yi nasara a zaɓen 2023.” Inji Elumelu.

Ishola-Balogun Fulani ne ya goyi bayan wannan roƙo da Elumelu ya yi. Daga nan Shugaban Kwamitin Amintattun PDP na riƙo, Adolphus Wabara ya nemi amincewar saura, kuma duk aka amince.

Amincewar ta zo daidai lokacin da Gwamna Nyesom Wike ke ƙumajin neman a cire a Ayu daga shugabanci a maye gurbin sa da ɗan Kudu.

PREMIUM TIMES ta buga labarin da a makon jiya Ayu ya bayyana cewa ba zai sauka ba.

A wani martani da ya maida wa Wike, ya ce “masu kiran na sauka daga shugabanci yarinta ke damun su”.

Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa Iyorchia Ayu ya bayyana cewa ba zai yi murabus daga shugabanci ba, saboda bai ga wani dalilin da zai sa a ya sauka ɗin ba.

Haka tsohon sanatan ya bayyana wa BBC Hausa a ranar Laraba.

Ayu na shan matsin-lamba daga ɓangaren Gwamna Nyesom Wike cewa saukar sa na daga cikin sharuɗɗan sulhu tsakanin Wike da Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP.

Rundunar Wike ta jajirce cewa tilas sai Ayu ya sauka a naɗa wa PDP shugaban jam’iyya ɗan kudu, tunda Ayu da Atiku Abubakar duk ‘yan Arewa ne.

Gwamnonin kudu na PDP na ƙorafin yadda ba a yi rabon muƙamai na PDP bisa adalci ba.

Sannan kuma wasu shugabannin PDP na zargin Ayu da nuna goyon baya ƙarara ga Atiku Abubakar a lokacin zaɓen fidda-gwani.

Sai dai kuma a ranar Laraba Ayu ya ce masu kiran ya sauka yara ne a cikin jam’iyya, ba su ma san yadda aka kafa PDP ba.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda taron neman sulhu ya wakana tsakanin Wike da Atiku, kwanan baya a birnin Landan.

Martanin Ayu:

Ya ce an zaɓe shi ne fa a ƙarƙashin ƙa’idoji da sharuɗɗan da jam’iyyar PDP ta gindaya.

“Shugabannin jam’iyya kafin zaɓen shugaba sun ce babu ruwan su da yin la’akari da inda shugaban jam’iyya ya fito idan an zo zaɓen fidda gwani na ‘yan takarar shugaban ƙasa.

“An zaɓe ni na yi shugabancin shekaru huɗu, kuma ban ma cika ko da shekara ɗaya a ofis ba. Zaɓen Atiku Abubakar ɗan takarar shugaban ƙasa bai shafi kujerar da shugaban jam’iyya ke kai ba. Na ci zaɓe bisa ƙa’idojin da jam’iyya ta shimfiɗa.

“Na maida hankali wajen yin aiki na. Kuma ban damu da masu surutai marasa kan-gado ba.” Cewar Ayu.

Da aka tambaye shi ba ya ganin rikicin da ake yi da ɓangaren Wike zai iya haifar wa PDP rashin nasara a zaɓen 2023, sai Ayu ya ce, “da ni aka kafa PDP, saboda haka wasu tsagerun yara da ba su ma san yadda jam’iyyar ta Keto daji har ta kawo yau, ba su isa su haifar wa jam’iyyar da matsala ba.

Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin tsauraran sharuɗɗan da Wike ya gindaya idan ana so a shirya.

Bayanan abin da ya faru tsakanin ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP Atiku Abubakar da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas, a taron neman sulhun da su ka yi a Landan, a ranar Alhamis sun fito fili Premium Times ta damƙe.

An taron neman sulhu ɗin ne a otal ɗin Lane Carlton Hotel. Daga cikin zaratan ɓangaren masu goyon bayan Wike, waɗanda suka raka shi zaman sulhun akwai Gwamna Seye Makinde na Jihar Oyo, Samuel Ortom na Jihar Benuwai, Okezie Ikpeazu na Jihar Abiya. Shi kuma Atiku ya na tare da Gwamna Ahmadu Fintiri na Jihar Adamawa.

Taron dai ya zo sa’o’i kaɗan bayan Wike ya gana da tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo da kuma Shugaban Jam’iyyar LP, Peter Obi duk a Landan ɗin. Dama kuma a ranar Litinin ɓangaren Wike ya gana da ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, wanda shi ma kamar Obi ya ke ƙoƙarin maida Wike ɓangaren sa, domin cin roba daga rigimar cikin gidan PDP, wadda ta rincaɓe tun bayan kammala zaɓen fidda-gwani.

Majiyar PREMIUM TIMES ta ce ɓangaren Wike ya shaida wa Atiku cewa matakin farko kafin a daddale yin sulhu ɗin tukunna, har Wike ya goyi bayan Atiku, sai Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Iyorchia Ayu ya sauka, a gaggauta maye gurbin sa da ɗan kudu.

Sun ce Wike da jama’ar sa ba za su taɓa goyon bayan ɗan takarar shugaban ƙasa daga Arewa sannan kuma shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa shi ma daga Arewa.

Ɗaya daga cikin gwamnonin ne ya yi magana a madadin sauran, ya ce wannan sharaɗi na farko su na so a gyara shi ne domin a yi adalci wajen rabon muƙamai. Kuma su na so a gyara da wuri kafin kusantowar zaɓen 2023.

Sannan kuma sun zargi Ayu da rarraba kai ko raba haɗin kan jam’iyya, maimakon kallon da ake yi masa wai wani mai haɗa kan PDP.

Ɓangaren Wike ya ce tun da aka kafa PDP ba a taɓa yin shugaban jam’iyya wanda ya rarraba kawunan ‘yan jam’iyya kamar Ayu ba.

Sun ce maimakon Ayu ya tashi ya nemi haɗin kan kowane ɓangare da sauran hasalallun da ba a yi wa adalci ba, sai ya ƙirƙiri sabon ra’ayin raba kawuna ta hanyar rungumar shugabannin da babu adalci da raba-daidai a cikin sa.

Wike dai ya zargi Ayu da nuna goyon bayan Atiku ƙarara a lokacin zaɓen fidda-gwani.

Ɓangaren Ayu ya ci gaba da cewa tilas Atiku ya tashi ya gyara rashin adalcin da aka yi wajen rabon muƙamai na shugabancin PDP, ta yadda tun a nan idan ya yi haka, to zai nuna da gaske ya ke yi zai iya haɗa kan ‘yan Najeriya kenan idan ya zama shugaban ƙasa.

Majiyar ta ce shi kuma Atiku ya yarda tabbas akwai ɓangarancin miƙa manyan muƙaman PDP a Arewa, to amma ya yi togaciya da cewa dokar PDP ta nuna idan shugaba ya sauka, ba za a iya yin gyaran da su ke so a yi ba, domin idan Ayu ya sauka, wanda zai maye gurbin sa ɗin ma Mataimakin Shugaban Jam’iyya ne na Ƙasa, kuma shi ma ɗan Arewa ɗin ne dai.

Sai dai kuma ɓangaren Wike sun tunatar da Atiku cewa a lokacin da shugaban PDP Okwesilieze Nwodo ya yi murabus cikin 2011 bayan an zaɓi Goodluck Jonathan ya zama shugaban ƙasa, ai ba a ɗauki mataimakin shugaban jam’iyya wanda shi ma a lokacin ɗan kudu ba ne.

Bayan an yamutsa gashin baki sosai a wurin taron, Atiku ya nemi su ɗan ba shi lokaci domin ya tuntuɓi manyan jam’iyya sannan ya waiwaye su.

Majiya ta ce wannan batun ne kaɗai aka tattauna a wurin taron, amma ba a tattauna sauran rashin jituwar da ke tsakanin Wike da Atiku ba.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news