Labarai

RUNDUNAR ATIKU A BENIN: ‘Zan ƙara wa jihohi da ƙananan hukumomi ƙarfin iko’ idan na zama shugaban kasa – Atiku

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa idan aka zaɓe shi, gwamantin sa za ta ƙara wa jihohi da ƙananan hukumomi ƙarfin iko, domin a samu ci gaba a faɗin ƙasar nan.

Atiku ya bayyana haka a rangandin yaƙin neman zaɓen PDP a Benin, babban birnin Jihar Edo. Saboda haka ne Atiku ya ce wa al’ummar jihar kada su bari wannan dama da garaɓasar ta wuce su. Don haka su zaɓi PDP a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Atiku ya ce ya yi nazarin cewa idan aka ƙara wa jihohi da ƙananan hukumomi ƙarfi, ci gaba zai fi saurin zuwa cikin garuruwa da yankunan karkara.

Jiga-jigan PDP da dama sun halarci rangadin kamfen ɗin, inda a ci gaba da jawabin Atiku ya ce zai ƙirƙiro ‘yan sandan jihohi domin shawo kan munin da matsalar tsaro ta yi a faɗin ƙasar nan.

“Mun yi alƙawarin dawo da tsaro a ƙasar nan, da mu dawo da kima da martabar jami’an tsaro, ta yadda kowa za iya fita ya je gona ya yi noma ba da wata fargaba ba.

“Za mu jibge ‘yan sanda kan tituna kuma mu wadata su da kayan aiki. Za mu ƙirƙiro ‘yan sandan jihohi, kuma za mu ƙara wa jihohi da ƙananan hukumomi ƙarfin iko ta yadda ci gaba zai fi saurin kaiwa garuruwa da yankunan karkara.” Inji Atiku.

Atiku ya bayyana ajandar sa guda biyar: farfaɗo da tattalin arziki, yadda masana’antu za su dawo su ci gaba da aiki.

Ya ce gwamnatin sa za ta samar da matasa aikin yi ta hanyar bijiro da masu zuba jari su ka kafa masana’antu.

Atiku ya dira Benin bayan dawowar sa daga Turai, inda ya fice kwana ɗaya bayan kai wa rundunar sa sunƙuru a taron Kaduna.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda Atiku ya fice Turai ‘domin hadar-hadar kasuwanci’.

Labarin dai ya na ɗauke da cewa ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, kuma tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya lula ƙasashen Turai domin yin wata ganawar hada-hadar kasuwanci.

Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran sa Paul Ibe ya fitar a ranar Laraba, ya ce Atiku ya tafi ne domin ganawa da wasu shugabannin wani kamfani dangane da ci bayan da aka samu sanadiyyar ɓarkewar cutar korona.

Atiku ya fice daga Najeriya kwana ɗaya bayan kallama taron Kaduna da kuma kamfen inda aka tabbatar da rahotonnin cewa wasu ɓatagari sun kai hari a wurin gangamin PDP.

Yayin da wasu ke ƙorafin cewa bai kamata Wazirin Adamawa ya fice zuwa Turai domin yin kasuwanci ko biyan wata buƙata ta shi shi kaɗai ba, a gefe ɗaya kuma wasu na yaɗa ji-ta-ji-tar cewa ya suma a wurin kamfen ne, shi ya sa aka garzaya da shi Turai bayan ya farfaɗo.

A ranar Laraba an riƙa watsa wani bidiyo inda aka nuno Atiku tare da Bukola Saraki, Daniel Bwala da Dino Melaye su na zaune ɗakin cin abinci da kuma wasu Turawa a gefe, waɗanda aka ce su ne abokan mu’amalar kasuwancin.

Dangane da harin da aka kai wurin kamfen ɗin Atiku a filin wasa na Ranchers Bees a Kaduna, da yawa sun ɗora laifin kan Gwamnatin APC a Kaduna da kuma Sanata Uba Sani ɗan takarar gwamnan Kaduna na APC.

PDP dai za ta ci gaba da kamfen a cikin wannan makon a Jihar Edo. Ba a sani ba ko Atiku zai dawo kafin lokacin, domin sanarwar fitar da ba ta bayyana kwanakin da zai yi a Turai ba.


Source link

Related Articles

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button